170208-Matakan-kasar-Sin-na-inganta-harkokin-noma-da-raya-karkaka.m4a
|
Wannan shi ne karo na 14 kana na farko a shekarar 2017 da gwamnatin kasar Sin ta fitar da takarda, da ta shafi harkokin raya kauyuka da aikin gona, da kuma bunkasa rayuwar manoma.
Takardar ta kuma jaddada bukatar daidaita huldar da ke tsakanin gwamnati da kasuwanni, da kuma moriyar sassa daban daban. Don haka ta ce kamata ya yi a fuskanci kalubalen da aka sanya gaba, don ingiza gyare-gyaren.
Bugu da kari, takardar ta bayyana aniyar gwamnati ta karfafa gwiwar daliban da suka kammala karatunsu a kasashen ketare su fara tafiyar da harkokin kasuwanci da za su taimaka wajen bunkasa yankunan karkara.
Haka kuma za karfafawa masu zuwa cin rani da su koma yankunan karkaka su fara harkokin kasuwanci, ko horas da mutane dabarun noma na zamani.
Masana na bayyana cewa, wannan mataki ya zo a lokacin da ya dace, duba da muhimmancin samar da isashen abinci ga al'ummar kowace kasa. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanisu Chen)