in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane 5 a cibiyar Islama dake Quebec
2017-01-30 15:58:35 cri
Tashar watsa labarai ta kasar Canada CBC, ta ce a kalla mutane 5 ne suka rasa rayukan su baya ga wasu da dama da suka jikkata, yayin wani hari da aka kaddamar a cibiyar Islama ta birnin Quebec dake kasar.

CBC ta rawaito hukumar 'yan sandan birnin na Quebec na cewa, wasu mahara dauke da bindigogi ne suka bude wuta a cibiyar, da misalin karfe 8 na daren Lahadi bisa agogon wuri.

Shaidun gani da ido sun ce an tsafke mutane biyu da ake zargi da hannu a aukuwar harin, kuma tuni 'yan sanda suka killace wurin da lamari ya auku.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China