in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ci gaba da zama ginshikin ci gaban tattalin arzikin duniya
2017-02-03 14:10:39 cri

Wasu alkaluma da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a kwanakin baya, sun nuna cewa, ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin a shekarar 2016 ya kai RMB biliyan 74412.7, adadin da ya karu da kashi 6.7 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2015.

Baya ga wadannan alkaluma sama da kashi 90 cikin 100 na attajiran kasar Sin sun nuna tabbaci game da makoma da ingancin tattalin arzikin kasar.

Haka kuma, a rubu'in farko na shekarar 2016, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kaso 6.7 cikin 100, kamar yadda masu sharhi suka yi hasashen cewa, a shekarar da ta gabata, tattalin arzikin kasar ta Sin zai bunkasa da kaso 6.7 cikin 100, karuwar da ta dara ta manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.

Wannan hasashe ya zo dai-dai da hasashen da asusun ba da lamuni na duniya IMF da sauran hukumomin kudi na kasa da kasa da wasu masana tattalin arziki a ciki da wajen kasar suka yi game da bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin na kaso 6.7 cikin 100.

Masu sharhi na cewa, wannan ba zai rasa nasaba da kwararan matakai da mahukuntan kasar suka dauka game da inganta tattalin arzikin kasar ba, wadanda suka hada da sassauta dokokin zuba jarin waje a cikin kasar, samar da kayayyakin fasahohi na zamani da sabbin ayyukan yi ga mutane fiye da miliyan 13 a kowace shekara a cikin shekaru hudu a jere da suka gabata.

Bayanai na nuna cewa, kasar Sin ta ba da gudummawar kaso 33.2 cikin 100 na bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma sabbin matakan da kasar ta dauka na raya tattalin arzikinta, sun taimaka mata wajen canjawa daga tattalin arzikin da ya dogara ga fitar da kayayyaki da zuba jari, zuwa tsarin tattalin arziki mai dorewa wanda yake kara samar da kayayyaki, hidima da kuma kirkire-kirkire. (Ahmed, Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China