in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da shugaban Sin ya kai kasar Switherland
2017-01-26 15:21:45 cri

A kwanakin baya ne wato daga ranar 15 zuwa 18 ga watan Janairun shekarar 2017, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai ziyara kasar Switherland, ziyararsa ta farko zuwa ketara a wannan shekara. Kuma a yayin wannan ziyara ce shugaba Xi ya halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya na Davos.

A lokacin wannan ziyara, shugaba Xi ya ziyarci ofishin MDD da ofishin hukumar lafiya ta duniya da kuma hedkwatar kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya dukkansu da ke Geneva. Ya bayyana a jawaban da ya gabatar yayin wannan ziyara wadda ta janyo hankalin kasa da kasa cewa, abu mafi muhimmanci shi ne a kara kokari tare domin kubutar da tattalin arzikin duniya daga mawuyacin halin da yake ciki. kuma wajibi ne kasashen duniya su hada kai domin bullo da wani sabon nau'i na hadin gwiwa da taimakon juna a tsakaninsu, ta yadda za a tabbatar da burin samun nasara tare da cin gajiyar nasarorin da duniya ta samu, wadda daga karshe za a samu wadata tare. Bugu da kari, ya jaddada bukatar kara bunkasa ciniki maras shinge da zuba jari a fadin duniya, tare kuma da yaki da manufar ba da kariya ga cinikayya.

Shugaba Xi ya sake nanata matsayin Sin na mutunta 'yancin kasashe daban-daban, da kokarin samarwa kasashe damammaki bisa adalci, da yin hakuri gami da bude kofa ga juna ta yadda za a taimakawa kasashe daban-daban su inganta dangantakarsu ta diflomasiyya. Haka kuma ya ce kamata ya yi a yi watsi da babakeren da wata kasa ko wasu kasashen ke nunawa. Kasashe daban-daban su ne za su samar da makomar duniya, su ne za su kafa ka'idojin duniya, su ne za su shiga a dama da su a wajen tafiyar da harkokin duniya, su ne kuma za su amfana daga nasarorin da duniya ta samu baki daya.

Jawabin shugaban ya kuma tabo batutuwan da suka shafi tabbatar da tsaro, da habaka tattalin arziki, da yin musanyar al'adu da sauransu. Masu fashin baki na cewa, jawabin shugaba Xi ya saka jaddada matsayin kasar Sin na martaba 'yancin kasashe daga dukkan fannoni da kuma kokarin Sin na samar da duniya mai zaman lafiya da wadata. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China