in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Nijeriya a shekarar 2016
2017-01-25 15:13:08 cri

Jama'a assalam alaikum! Barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan sabon shiri na SIN DA AFRIKA, ni ne Saminu Alhassan nake gataba muku da shirin daga nan sashin Hausa na gidan rediyon kasar Sin CRI.

A watan Agusta na shekarar 2016 da ta gabata, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata sabuwar hanyar jirgin kasa ta fasinjoji tsakanin birnin Abuja da jihar Kaduna. Wani babban kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CCECC shi ne ya dauki nauyin shimfida hanyar. Wannan layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna, wani sashi ne dake cikin babban layin dogo na zamani wanda za'a shimfida daga birnin Lagos har zuwa jihar Kano dake arewacin Najeriya.

Layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna, jimillar tsawonsa ya kai kilomita 187, akwai tashohi guda 9 gaba daya a kan wannan layi. Gina wannan layin dogo ba ma kawai zai raya tattalin arzikin wannan yanki ba, har ma zai samar da dimbin guraben ayyukan yi ga mutanen Najeriya. Kaza lika, zai taimakawa kasar Sin wajen fitar da kaya da na'urorin zamani na jirgin kasa zuwa kasashen ketare, ta yadda za'a inganta hadin-gwiwar Sin da Najeriya a fannin tattalin arziki da kasuwanci da kuma sufuri.

Wakilin mu Murtala Zhang ya halarci bikin kaddamar da wannan layin dogo, bari mu waiwaye rahoton da ya hada mana a lokacin:

Ban da haka kuma, ana ci gaba da raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, kamar yadda aka ambata cikin shirye shiryen mu da suka gabata, dangane da bunkasuwar hadin gwiwar Sin da Nijeriya a fannin masana'antu da ayyukan noma har ma da musayar al'adu a tsakanin sassan biyu, lamarin da ya sa mutanen Nijeriya ke kara sha'awar harkokin kasar Sin. Abokiyar aikinmu dake birnin Abuja malama Amina Xu ta tattauna da masanin harkokin kasar Sin na jami'ar Abuja Sheriff Ghali Ibrahim, kan wasu batutuwan dake shafar tattalin arzikin kasa ta Sin. Ga yadda tattaunawar ta su ta kasance:

Don gane bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Nijeriya da kuma hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban, babu shakka, kasashen biyu za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a wannan shekara, lamarin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya kai ziyarar aiki Nijeriya, tun da farkon shigar shekarar ta 2017, inda ya mika gaisuwar shugaba Xi Jinping ga shugaba Muhammadu Buhari a wannan sabuwar shekara.

Haka kuma, a yayin ganawarsa da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya kuma nuna fatan kasar Sin na ci gaba da hadin gwiwar dake tsakaninta da Nijeriya wajen aiwatar da sakamakon dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, kana da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu kan ayyukan noma, gina layin dogo, hakar ma'adinai da dai sauransu, ta yadda Nijeriya za ta kyautata kwarewarta wajen neman bunkasuwa da kanta. A nasa bangare kuma, shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa, a lokacin da ya kai ziyarar aiki a kasar Sin a shekarar da ta gabata, ya cimma matsaya daya da shugaba Xi Jinping, kan zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, sa'an nan, Nijeriya ta dauki matakai da dama domin aiwatar da harkokin da suka cimma ra'ayi daya yadda ya kamata, yayin da ake sa ran ci gaba da zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban a nan gaba.

Dangane da wannan lamarin, ministan harkokin ma'adinai na kasar Nijeriya, da gwamnan jihar jigawa sun taba tattauna da ni da kuma wakiliyar sashenmu Amina Xu, kan yadda za a raya hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin a nan gaba cikin shirinmu. Ga kuma waiwaye na yadda tattaunawar ta kasance:

To, madalla, muna kuma fatan hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasar Nijeriya a shekarar 2017 zai kara fadada yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga zurfafa fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, yayin da ake samun ci gaba tare. Da haka kuma zan ja akalar shirin na mu na yau na SIN DA AFIRKA, da fatan za ku kasance da mu a mako mai zuwa, domin jin mu dauke da wani sabon shirin, ku huta lafiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China