in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yaba da ziyarar farko da shugaba Xi ya kai a shekarar 2017
2017-01-20 11:08:47 cri

Jiya Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki uku da ya kai kasar Swiszerland, kuma har ya dawo nan birnin Beijing lami lafiya. MDD, da wasu kungiyoyin kasa da kasa, da jakadun kasashen duniya dake wakilci a Geneva, da ma fannoni daban daban, musamman ma fannin tattalin arziki baki daya sun yaba wannan ziyara matuka.

Shugaba Xi Jinping ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Swiszerland tsakanin ranakun 15 zuwa 18 ga wannan wata, yayin ziyarar tasa, ya kuma halarci taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na bana, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi, kana ya kai ziyara a ofishin kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasashen duniya, da na hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, daga baya ya halarci taron kolin da aka shirya domin tattauna batutuwan dake shafar makomar bil adama, inda nan ma ya gabatar da wani jawabi mai taken "Hada kai tare domin kafa makoma mai haske ga bil adama".

A ranar 18 ga wata, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya taba bayyana wa manema labarai cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping ta nuna mana cewa, kasar Sin tana nacewa ga manufar hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa, shi ma ya yabawa kasar Sin cewa, tana taka muhimmiyar rawa a wannan fannin. Yana mai cewa, "Ina ganin cewa, jawaban da shugaba Xi ya gabatar sun sake jaddada matsayin kasar Sin game da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, hakika kasar Sin ta ba da gudummuwa a wannan fannin."

Babban sakataren rukunin sadarwa ta kasa da kasa Zhao Houlin shi ma ya yaba da ziyarar Xi, inda ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna fuskantar yanayi maras tabbas, jawaban da shugaba Xi ya gabatar a dandalin kasa da kasa a madadin kasar Sin sun kara karfafa zukatun al'ummomin kasashen duniya. Ya ce, "Yayin ziyararsa ta farko a bana shugaba Xi ya halarci dandalin tattalin arzikin duniya na Dawos, hakan ya nuna cewa, shugaba Xi yana mai da hankali sosai ga batun tattalin arzikin duniya da ci gaban zaman takewar al'ummar kasashen duniya, kana yayin ziyarar tasa, ya gabatar da jawabai domin nuna matsayin kasar Sin da kuma nunawa sauran kasashen duniya irin sakamakon da kasar Sin ta samu. Yanzu kasashen duniya suna fuskantar yanayi maras tabbas, da manyan sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki, lamarin da haifar da zaman zulumi, don haka, akwai bukatar a yiwa duniya karin haske, a daidai wannan lokaci, ziyarar shugaba Xi a farkon shekarar 2017 ta cimma nasara, saboda ta kara karfafa zukatunsu."

Jakadar kasar Mali dake wakilci a Geneva Thiam ta bayyana cewa, a cikin jawaban da shugaba Xi ya gabatar, ya nuna wa al'ummomin kasashen duniya matsayin kasar Sin game da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa, ko shakka babu ziyararsa ta samu cikakkiyar nasara.

Yayin da shugaba Xi yake gabatar da jawabi mai taken "Hada kai domin samar da makoma mai haske ga bil adama" a fadar "Palace of Nations" dake Geneva, mahalarta taron sun yi tafi har sau 30. Mataimakin babban jami'in hukumar ciniki ta duniya WTO Yi Xiaozhun ya bayyana cewa, jawabin shugaba Xi ya sake nanata cewa, bil adama a fadin duniya suna da makoma guda, kana ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufar samun ci gaban tattalin arziki tare da daukacin kasashen duniya, Yi Xiaozhun yana ganin cewa, tunanin shugaba Xi ya nuna mana ainihin ma'anar makomar bil adama. Ya ce, "Shugaba Xi ya tabbatar da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufar samun ci gaban tattalin arziki tare da sauran kasashen duniya, wannan tunani shi ne ainihin ma'anar makomar bil adama, duk da cewa, ana fama da wasu kalubale a fannoni daban daban, amma bai kamata ba a daina yin kokari, ina ganin cewa, duk wadannan dalibai da suka saurari jawabi ne suka ta yin tafi, saboda sun yarda da matsayin kasar Sin."

Kazalika, babban manajan bankin CCB wato bankin raya tattalin arzikin kasar Sin, reshin birnin Zurich wanda shi ne reshin bankin kasar Sin na farko da aka kafa a Swiszerland Gong Weiyun ya bayyana cewa, a cikin jawabin da ya bayar a dandalin Dawos, shugaba Xi ya gabatar da ra'ayoyi masu muhimmnaci guba biyu, wadanda za su taimaka matuka ga cinikin waje na kasar Sin, wato na farko shi ne kasar Sin za ta nace ga manufar samun ci gaban tattalin arziki tare da sauran kasashen duniya, tare kuma da ba da jagoranci a fannin, na biyu, kasar Sin za ta kara yin kokari game da shirin "ziri daya da hanya daya", kuma za ta shirya taron koli a watan Mayu mai zuwa domin tattauna hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa. Gong Weiyun ya kara da cewa, manufofin da kasar Sin ta ke aiwatarwa sun samar da tabbaci ga kamfanonin kasar yayin da suke kokarin shiga kasuwannin kasashen duniya, bankuna ma za su ci gajiya daga wadannan manufofi.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China