Kakakin rundunar, Ayodele Famuyiwa, ya ce za a gudanar da binciken ne domin kare sake aukuwar lamarin, tare da sanin dalilai da kuma abubuwan da suka janyo kai harin.
Mutane akalla hamsin da biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu dari da ashirin suka jikkata, a harin da tuni rundunar sojin ta ayyana a matsayin kuskuren aiki.
Rundunar sojin Nijeriya ta ce al'amarin ya auku ne, bayan ta samu wani rahoton sirri dake cewa, 'yan kungiyar Boko Haram na sake hade kansu a garin da sansanin yake.
Har ila yau, Ayodele Famuyiwa, ya ce rundunar sojin saman ta kafa wani kwamiti mai kunshe da manyan hafsoshi, domin gudanar da bincike kan harin, baya ga shaidun gani da ido ashirin da ake da su.
Sannan, an ba ayarin masu binciken damar gayyatar duk wanda ke da shaida kan al'amarin, inda ya ce, kwamitin zai mika rahotonsa ranar ko kafin 2 ga watan Fabreru mai zuwa.(Fa'iza Mustapha)