in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufofin kasar Sin game da hadin kan tsaro a yankin Asiya da Fasifik
2017-01-19 12:00:22 cri

A ranar Laraba 11 ga watan Janairun shekarar 2017 ne, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani wadda ke bayyana manufofin kasar game da hadin kan tsaro a yankin Asiya da Fasifik.

Takardar ta yi bayanin cewa, yankin Asiya da Pasific yana da matukar muhimmanci a tsarin duniya.

Baya ga haka, takardar ta nuna cewa, kasar Sin tana da wani dauwamammen ra'ayin tsaro da hadin kai na bai daya, tare kuma da bin hanyar hada kai, da yin musaya da samun nasara tare a kokarin tabbatar da tsaro a yankin.

Ban da wannan kuma, takardar ta yi bayani game da dangantakar dake tsakanin Sin da wasu muhimman kasashe da ke yankin, ciki har da Amurka, Rasha, India, Japan da dai sauransu, ta kuma bayyana cewa, kasar Sin tana kokarin bunkasa dangantakar abokantaka ta hadin kai tsakaninta da sauran kasashen yankin.

Kana kuma takardar ta bayyana matsayi da kuma manufofin kasar Sin kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi matsalar nukiliyar zirin Koriya, na'urorin kakkaba makamai masu linzami, kasar Afghanistan, yaki da ta'addanci da kuma tsaron teku da dai sauransu.

Bayan haka kuma, takardar ta bayyana matakan da kasar Sin ta dauka a fannin hadin kan tsaro a yankin, kamar shiga ayyukan ceton bala'u, yaki da ta'addanci, yaki da masu aikata laifufuka na kasa da kasa, tsaron yanar gizo ta intanet, tsaron teku, hana yaduwar makamai da kuma kwance damarar soja da dai sauransu.

A karshe takardar ta ce, jama'ar kasar Sin na kokarin cimma burinsu na inganta rayuwar al'umma, don haka kasar Sin za ta kara kawo wa yankin damar hadin kai da moriya. Wannan a cewar masana ya kara jaddada matsayin kasar Sin na tabbatar da tsaro da wadata a duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China