in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Nijeriya bisa fannin musayar al'adu a shekarar 2016
2017-01-17 15:22:32 cri

Jama'a masu sauraro Assalam Alaikum! Barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku, a wannan sabon shiri na SIN DA AFRIKA. A yau ni ne Saminu Alhassan zan gabatar muku da shirin daga nan sashin Hausa na gidan rediyon kasar Sin CRI.

Cikin shirinmu na makon da ya wuce, mun waiwaye wasu batutuwa da suka wakana a shekarar bara, game da bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasar Nijeriya, musamman a fannonin siyasa, da tattalin arziki. Kamar dai yadda muka sani shugabannin kasashen Sin da Nijeriya, sun kaiwa juna ziyara sau da dama, domin habaka ayyukan da suka jibanci dangantakar su yadda ya kamata.

A cikin shirinmu na yau kuma, za mu yi duba ne kan irin nasarorin da aka samu a fannin bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannin musayar al'adu, lamarin da yake daukar muhimmiyar ma'ana, wajen karfafa zumunci, da kuma fahimtar juna dake tsakanin al'ummoni da gwamnatocin kasashen biyu, matakin dake ba da taimako ga ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban.

Amma kafin hakan bari mu leka taskar mu ta wannan shiri, domin kawo wa mai sauraro bitar wata ziyara da babban mai shari'a a kotun tarayyar Najeriya Ibrahim Auta ya kawo nan birnin Beijing cikin watan Oktobar shekarar ta bara, inda ya halarci taron karawa juna sani na kasa da kasa, game da kalubalolin da ake fuskanta a fannin dokoki, a yayin da ake zuba jari, da ma sauran harkokin tattalin arziki da cinikayya. A yayin wannan ziyara dai mai shari'a Auta, ya tattaunawa da masanan a wannan fanni, kan harkar dokoki masu alaka da tattalin arziki da zuba jari, lamarin da kara haskaka halin da ake ciki tsakanin kasar Sin da kasar Nijeriya a wannan fanni.

Kaza lika kuma, hakan ya taimaka wajen karfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban, musamman ma duba da cewa, rashin fahimtar dokoki na daya daga manyan matsala da kamfanonin kasar Sin ke fuskanta a fannin zuba jari a kasashen wajen.

Yanzu kuma bari mu waiwayi fannin musayar al'adu, inda a baran dai, wata tawagar wakilan matasan Nijeriya ta iso nan kasar Sin a watan Agusta na shekarar ta bara, domin halartar bikin matasan Sin da Afirka na shekarar 2016, wanda da ya zama wani bangare na aiwatar da shirin ziyarar juna a tsakanin matasan Sin da Afirka, wanda da aka cimma kudurin aiwatarwa, yayin taron kolin Johannesburg na FOCAC da ya gudana a watan Disambar shekarar 2015.

Rahotanni sun nuna cewa, gaba daya wakilai 188 daga kasashen Afirka 18 ne suka halarci wannan shagalin biki na birnin Guangzhou, wanda ya baiwa matasan damar musayar ra'ayoyi da takwarorinsu su 200, wadanda ke zaune a lardin Guangdong, a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu, da hidimar zaman takewar al'umma da dai sauransu.

Haka kuma, kafin gudanar wannan shagali na birnin Guangzhou, an yi bikin wake-wake da raye-raye na matasan kasashen Asiya da Afirka karo na farko a nan birnin Beijing, inda matasa 600 daga bangarorin siyasa, da kafofin watsa labaru, da kasuwanci, da nazari daga kasashen Asiya, da na Afirka 36, suka taru a nan kasar Sin domin su tattauna da juna, su kuma kara fahimtar juna a tsakaninsu. Bayan hakan ne kuma, wakilan 188 daga kasashen Afirka, suka ci gaba zuwa birnin Guangzhou, inda aka yi shagalin biki na matasan na Sin da Afirka a can.

Wakiliyar sashen mu Kanda Gao ta halarci bikin da aka yi a birnin na Guangzhou, inda ta kuma zanta da wasu wakilan matasan kasar Nijeriya, ga kuma yadda tattaunawar ta su a wancan lokaci ta kasance.

To, madalla, muna kuma fatan mu'amala a tsakanin kasar Sin da kasar Nijeriya a shekarar 2017 za ta kara fadada yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga zurfafa fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban, yayin da ake habaka hadin gwiwa, da haka kuma za ja akalar shirin na mu na yau na SIN DA AFIRKA, da fatan za ku kasance da mu a mako mai zuwa, domin jin mu dauke da wani sabon shirin, ku huta lafiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China