in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta saukaka takunkuminta a kan Sudan
2017-01-14 14:04:07 cri
A jiya Juma'a ne, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, sakamakon matakan da kasar Sudan ta dauka na yaki da ta'addanci da kyautata harkokin shigar da agajin jin kai cikin kasar, za ta saukaka takunkumin da ta sanya mata a wasu fannoni.

Shugaban Amurka Barack Obama ne ya sanar da haka, inda ya ce, idan har kasar ta Sudan ta ci gaba da samun ci gaba a fannonin yaki da ta'addanci da dakatar da rikice-rikice a yankin Darfur da kuma kyautata harkokin jin kai, to Amurka za ta soke takunkumin da ta sanya mata a wasu fannonin da suka hada da haramcin cinikayya daga ranar 12 ga watan Yuli da ke tafe.

Sai dai, ya ce za a ci gaba da sanya wa kasar takunkumi ta fannonin da suka jibanci yadda take cikin jerin sunayen kasashen da ke goyon bayan ta'addanci da Amurka ta lissafa, da kuma batun Darfur.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sudan a jiya Juma'a, ta fitar da sanarwar cewa, kasar na maraba da kuduri na gwamnatin Amurka, kudurin da ke shaida ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen biyu, wanda kuma nasara ce da kasashen biyu suka cimma ta fuskar hadin gwiwa a kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa.

Sanarwar ta ce, Kasar Sudan za ta ci gaba da hada gwiwa da tattaunawa da Amurka, har zuwa lokacin da za ta cire ta daga jerin sunayen kasashen da ke goyon bayan ta'addanci.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China