170110Bunkasuwar-hadin-gwiwar-Sin-da-Nijeriya-bisa-fannin-siyasa-da-tattalin-arziki-a-shekarar-2016-maryam.m4a
|
Cikin shekarar 2016 da ta gabata, manyan jami'an tarayyar Najeriya daban daban sun kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin, domin habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da tarayyar Nijeriya bisa fannoni daban da dama. Cikin wadannan jami'ai dai hadda ministan harkokin ma'adinai Abubakar Bawa Bwari, wanda ya zo nan kasar Sin cikin watan Satumba, bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi masa, game da tattaunawa kan yadda za a raya hadin gwiwar kasashen biyu a fannin hakar ma'adinai.
Haka kuma, akwai wata tawagar wakilan Nijeriya da ta kunshi gwamnoni da dama da ta ziyarci wasu sassan kasar ta Sin, domin tattaunawa da takwarorinsu na kasar ta Sin kan yadda za a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, sun kuma ziyarci wasu kamfanonin kasar Sin da suka rigaya suka kulla dangantakar raya tattalin arziki da zuba jari a tsakaninsu da wadannan jihohi na Nijeriya.
Cikin gwamnonin da suka zo wannan kasa a watan Agustar da ya gabata dai hadda gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, da na jihar Katsina Aminu Bello Masari, da gwamnan jihar Plateau Simon Lalong.
A fannin manyan jami'ai kuwa akwai kwamishinan ma'aikatar gona na jihar Adamawa Alhaji Waziri Ahmadu da dai sauransu.