in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi kira ga Amurka da ta soke takunkumin da ta sanya mata
2017-01-08 13:58:22 cri
Gwamnatin kasar Sudan a jiya Asabar ta yi kira ga gwamnatin Donald Trump da za a rantsar nan ba da dadewa ba da ta sake tantance manufarta a kan kasar Sudan, kuma ta soke takunkumin da ta sanya mata a fannin tattalin arziki da zirga-zirga tun da wuri.

Ministan kula da harkokin waje da na cikin gida na kasar ta Sudan Kamal-Eddin Ismail a wata sanarwar da gwamnati ta fitar ya bayyana cewa, Sudan tana son hadin gwiwa da sabuwar gwamnatin kasar Amurka, don tabbatar da moriyarta.

A ranar 31 ga watan Oktoban shekarar bara, shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya sanar da tsawaita wa'adin takunkumin da kasarsa ta sanya wa Sudan da shekara guda, kuma a cewarsa, matakan da gwamnatin Sudan ke dauka da ma manufofinta na ci gaba da kawo barazana ga Amurka ta fannin tsaro da kuma harkokin diplomasiyya.

A cikin sanarwar, Kamal-Eddin Ismail ya yi suka ga bambancin da Amurka ke nuna wa kasar Sudan, inda ya ce, "sau tari ne muka bayyana wa Amurka bukatunmu na soke takunkumin da ta sanya mana, da kuma illolin da za mu fuskanta ta fannin zaman lafiya da tsaro idan ta tsawaita wa'adin takunkumin", za mu fuskanci illoli masu yawa a fannonin noma da masana'antu da zirga-zirga da ilmi da kiwon lafiya da ma manyan ababen more rayuwa idan har kasar Amurka ta ci gaba da sanya mana takunkumi.

A shekarar 1993, gwamnatin Amurka ta sanya kasar Sudan cikin jerin kasashen da ke tallafawa ta'addanci, kuma daga shekarar 1996 ta fara sanya wa kasar takunkumi.

Alkaluman da kasar Sudan ta samar sun shaida cewa, kasar ta Sudan tana fuskantar hasarar tattalin arziki da suka zarce dalar Amurka biliyan hudu a kowace shekara a sakamakon takunkumin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China