170104-Matsalar-hare-haren-taaddanci-a-duniya.m4a
|
A ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2017, tawagar UNAMI dake aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar Iraki, ta sanar da cewa, a watan Disamban shekarar 2016, wasu hare–haren ta'addanci da tashe-tashen hankula, sun yi sanadiyar mutuwar rayukan fararen hula 386, baya ga mutane 1,066 da suka jikkata.
Haka kuma a kasar Turkiya, mutane a kalla 39 ne suka mutu, kana wasu 40 suka jikkata, yayin da wani dan bindiga ya bude wutan a kan daruruwan mutane da ke shagulgulan murnar sabuwar shekara a wani gidan rawa da ke birnin Istambul.
Bugu da kari, wasu 'yan bindiga sun halaka jama'a a kasashen Somaliya da Najeriya da Nijar da wasu sassa na duniya, baya ga miliyoyin mutane da suka bar muhallansu, sakamakon tashe-tashen hankula dake da nasaba da ayyukan ta'addanci.
Masu fashin baki na cewa, wajibi ne kasashen yammacin duniya su guji tsoma baki a harkokin cikin gida, siyasa da sauran fannoni na sauran kasashe da sunan kare 'yancin bil-Adama ko tsarin demokiradiya.
Masu sharhin na ganin cewa, muddin ana bukatar cimma burin da aka sanya gaba na wanzar da zaman lafiya, wajibi ne a rika martaba 'yancin kasashe da dokokin kasa da kasa game da samar da tsaro da yaki da ayyukan ta'addanci a duniya. Haka kuma, suna al'umma suna da hakkin taimakawa mahukunta da muhimman bayanai da martaba dokar kasa daga dukkan fannoni. Wannan su ne matakan da idan har aka martaba su, hakika, za a samu zaman lafiya, tsaro da bunkasuwa a duniyarmu. (Ahmed,Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)