170103tawagar-sintiri-a-chengdu-maryam.m4a
|
Kwanan baya, wata tawagar sintiri ta mazauna unguwanni da aka kafa a birnin Chengdu na kasar Sin, ta fara yin suna a shafin intanet, sabo da mambobin tawagar 'yan kasashen ketare ne, ciki hadda Amurkawa, da Faransawa, da 'yan kasashen Australia, da Pakistan, da Ghana da kuma New Zealand da dai sauransu. Kaza lika, wasu daga cikinsu suna karatu a nan kasar Sin, wasu suna aiki a kamfanonin kasar, akwai ma wani dan shekaru 50 daga kasar Amurka, wanda yake koyar da Turanci a birnin na Chengdu.
An kafa wannan tawaga ne a unguwar Tong zi lin, dake yankin Wuhou na birnin Chengdu, bisa wani shirin da birnin ya tsara wa 'yan kasashen waje da suke zaune a Chengdu, wanda aka yiwa lakabi da "Gida a birnin Chengdu".
Shugaban tawagar Chris, wanda sunansa na Sinanci Zhang Rui ya bayyana cewa, dama ya yi karatu ne a nan kasar Sin har tsawon shekaru hudu, kuma yana da sha'awar taimaka wa Sinawa da 'yan kasashen ketare, wadanda suke zaune a unguwar ta Tong zi lin. Kana, a halin yanzu, dukkan mambobin tawagar suna aikin warware sabani tsakanin al'ummun unguwar, da kuma samar da taimako gare su, yayin da suka nuna bukatunsu ga kwamitin mazauna unguwar.
Shugabar kula da harkokin unguwar Tong zi lin Zhang Li, ta ce a halin yanzu, gaba daya akwai 'yan kasashen ketare sama da guda 2600 dake zaune a uguwar. Kuma a farkon shekarar bana, birnin Chengdu ya fidda shirin "Gida a birnin Chengdu", domin ganin wadanda suka zo daga kasashen ketare sun jin dadin zaman a birnin. Wannan shi ne dalilin kafa wannan tawagar sintiri ta mazauna unguwar 'yan kasashen ketare, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ta yadda za su ji dadin zamansu a birnin Chengdu, kamar yadda suke ji a gida.
Shugaban wannan tawaga Chris ya kware sosai a yaren Sinanci, a karon farko da ya zo kasar Sin a shekarar 2008, domin neman digirinsa na biyu a jami'ar sufuri ta Lanzhou, ya ce, ya fara koyon Sinanci tun daga wancan lokaci, kuma ya kan yi hira da sauran daliban ajinsa, lamarin da ya sa ya iya Sinanci sosai a halin yanzu. Kana, a watan Satumba na shekarar 2016, Chris ya koma birnin Chengdu domin neman digirinsa na uku a jami'ar kimiyya da fasahar kayayyakin lantarki.
A ranar 4 ga watan Oktoba na shekarar 2016, tawagar sintiri ta mazauna unguwanni ta fara aikinta a karon farko, inda suke kewaya unguwar, suna tattaunawa da mazaunan ta, da nufin jin ko akwai sabani a tsakaninsu, da ma wasu bukatu da suke da su. Haka kuma, tawagar tana da ofis, inda a kan buga musu waya idan mambobin tawagar ba su gane abin da Sinawa suke fada ba.
Chris ya ce, a kan hadu da Sinawa da suke sha'awa da kuma mamakin ayyukan da mambobin tawagar suke gudanarwa a wannan unguwa, amma ba sa iya tattaunawa da mambobin tawagar, balle ma su gaya musu matsalolin da suke fama da su. A ganin Chris, dukkan mambobin su, na fatan kara musaya tsakaninsu da mazauna unguwar 'yan kasashen ketare da Sinawa, ta yadda za a taimakawa juna yadda ya kamata.
Bugu da kari, ya ce, a baya ya taimaka wa wani malami mai koyar da Turanci a birnin Chengdu wajen neman wurin zama. Haka kuma idan akwai wasu da suke son zuwa yawon shakatawa a birnin Chengdu, ya kan ba su shawarwari na yadda za su cimma nasarar hakan.
Haka zalika, tawagar ta kuma kafa wani ajin koyon Sinanci a unguwar Tong zi lin, inda su kan koyar wa mutanen unguwar wadanda suka zo daga kasashen ketare Sinanci a ko wane mako, har ma su kan gayyaci sinawa da su shiga ajin domin koyar musu Sinanci.