in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta ce yankin Abyei mallakarta ce
2017-01-04 10:37:42 cri
Gwamnatin kasar Sudan ta sake nanata cewa, yankin Abyei da kasashen Sudan da Sudan ta kudu suke takaddama a kansa, mallakar ta ce,kamar yadda kungiyar AU da kotun kasa da kasa suka yi ittifaki a kai.

Ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a jiya Talata. Kalaman ministan na zuwa ne kwana guda bayan ziyarar da takwaransa na kasar Sudan ta kudu ya kai birnin Khartoum.

Minista Ghandour ya ce, yankin na Abyei ya fada bangaren Sudan ne, kamar yadda yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin kasashen biyu a shekarar 2005 ta tanada, ta hanyar la'akari da iyakokin kasashen biyu da aka shata a watan Janairun shekarar 1956.

Kasashen Sudan da Sudan ta kudu dai suna takaddama a kan yankin Abyei mai arzikin mai ne, yankin da galibin mazaunansa Larabawan Mesiria na Sudan ne da kuma kabilar Dinka Ngok daga bangaren Sudan ta kudu.

Kaso biyu bisa uku na rijoyoyin man kasar Sudan dai suna yankin Abyei ne, yankin da ya sha fama da rikici tsakanin kabilun biyu da kuma sojojin kasashen biyu, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China