170102-Mai-tsare-tsaren-tufaffi-da-kayayyakin-ado-yar-kabilar-Mongoliya-Bilkisu.m4a
|
Tufafi da kayayyakin ado wani muhimmin sashe ne na al'adun gargajiya. Tun kusan sama da shekaru dubu daya, 'yan kabilar Mongoliya na kasar Sin suka fara tsara tufaffi da kayayyakin ado da dama masu kyan gani kwarai. Gasar tufaffi da kayayyakin ado na kabilar Mongoliya da aka shirya a watan Yulin bana, ya jawo hankulan 'yan takara sama da 700 da suka fito daga kasar Sin da wasu kasashen ketare, ciki har da kasar Mongoliya da Rasha. Si Ri Ge Ma tana ma daya daga mahalarta gasar, wadda kuma ta samu lambr yabo ta biyu bisa tufaffi da kayayyakin ado da ta tsara, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani game da wannan mai tsare-tsare, yar kabilar Mongoliya.