in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun kwace dajin Sambisa daga hannun Boko Haram
2016-12-30 16:12:38 cri

A kwanakin baya ne shugaban Najeriya Muhammadu ya sanar da cewa, sojojin kasar dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, sun yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram daga babbar maboyarsu dake dajin Sambisa.

Shugaban na Najeriya ya taya sojojin kasar murna, bisa nasarar da suka samu na kwace dajin Sambisa wanda ya kasance babbar maboyar mayakan na Boko Haram.

Buhari ya ce, ya yi matukar farin ciki, kuma wannan abin alfahari ne da dakarun kasar suka nuna,na kwace dajin Sambisa wanda aka jima ana tsammani hakan, kuma shi ne maboya ta karshe na mayakan Boko Haram.

Shugaban ya kuma bukaci dakarun kasar da su cigaba da gudanar da aikinsu na fatattakar 'yan ta'adda da kuma kokarin ganin an kama wadanda suka arce, don gurfanar da su a gaban kuliya.

Masu fashin baki na cewa, wannan wata babbar nasara ce a yakin da dakarun kasar ke yi da 'yan ta'adda. Don haka, sun bukaci 'yan Najeriya da su taimakawa sojojin kasar da sauran jami'an tsaro da muhimman bayanai wadanda za su kai ga murkushe 'yan ta'addan baki daya.

Bugu da kari, masana na ganin cewa, wajibi ne mahukunta su tashi tsaye wajen samarwa dakarun kasar kayan aiki da fasohohi na zamani.(Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China