in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Duk da dimbin kalubalen da ta ke fuskanta, kasar Afrika ta Kudu na da yakinin za su zama tarihi
2016-12-30 09:55:06 cri

2016 za ta kasance wata shekarar da za ta shiga cikin tarihi a kasar Afrika ta Kudu, kasancewarta daya daga cikin shekaru da kasar ta fuskanci kalubale ta fuskar tattalin arziki da harkokin siyasa.

Kasar Afrika ta Kudu na ci gaba da fuskantar tsaiko a kokarin da take na habaka tattalin arzikinta. Bugu da kari, har zuwa yanzu, ba ta gama farfadowa daga matsalolin kudi da ta shiga a shekarar 2007 da 2008 ba, yayin da ficewar Birtaniya daga tarayyar Turai da saukar farashin kayayyakin da take fitarwa ke ci gaba da zame mata kalubale.

Haka zalika a fagen siyasa, inda take samun rarrabuwar kawuna a jami'iyyar ANC mai mulkin kasar, baya ga matsin lamba daga jam'iyyun adawa, tare da bakin jinin da shugaban kasar Jacob Zuma ya yi a idanun al'ummar kasar.

Duk da shigar da masu ruwa da tsaki da ta yi domin lalubo bakin zaren tare da samun dorewawar manufofin farfado da muhimman bangarori kamar na hakar ma'adanai, masana sun yi ammana cewa, har yanzu kasar ba ta gama farfadowa ba.

Matsalar tattalin arziki.

Bangaren hakar ma'adanan kasar da yake matsayin daya daga cikin wadanda aka albarkace su da ma'adanai a duniya, kuma kashin bayan tattallin arzikin kasar, na daya daga cikin bangarorin da suka fuskanci koma baya a bara.

Babban daraktan cibiyar hakar ma'adanai na kasar Afrika ta kudu Roger Baxter, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin cewa, bangaren hakar ma'adanai ya fuskanci gagarumin kalubale, Yana mai cewa, a cikin shekarar 2015 kadai, ya yi asarar sama da dalar Amurka biliyan biyu. Sannan, ya ci gaba da fuskantar kalubale a wannan shekarar da muke shirin ban kwana da ita.

Ya kara da cewa, farashin kayyayakin da kasar ke fitarwa ya ragu, sannan farashin kayayyaki a cikin gida ya yi tashin gwauron zabi, yana mai alakanta wannan matsala da farashin lantarki da ya gaza daidaituwa.

Ya kuma ce, a kowace shekara cikin shekaru biyar, kudin albashin ma'aikata na karuwa da kashi 10 cikin dari, haka zalika kudin kayayyaki.

Roger Braxter ya ce ana sa ran a sabuwar shekara mai kamawa, bangaren hakar ma'adanai zai mai da hankali wajen rage kudaden da yake kashewa, tare da kara inganta ayyunkansa domin samun damar tsayawa da kafarsa.

Ya ce dole ne Afrika ta Kudu, ta samar da nagartattun tsare-tsare, domin masu sha'awar zuba jari su samu kwanciyar hankali, ta yadda za su zuba jari mai nisan zango.

Roger Braxter wanda kwararre ne kan harkokin tattalin arziki, ya kuma ba da shawarar baza komar tattalin arzikin kasar maimakon dogaro a kan abu guda.

A nasa bangare, Babban Bankin Afrika ta Kudu ya yi hasashen cewa, zuwa shekarar 2018, matsalar hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar kudin kasar zai kai kashi biyar da rabi cikin dari.

Sai dai, duk da irin wadanan dimbin matsaloli, babban manajan sadarwa na kamfanin dake tallar kayayyakin da aka sarrafa a kasar, wato Brand South Afrika Manusha Pillai, ya yi imanin cewa, kasar ta yi kokari wajen shawo kan matsalolin da ta fuskanta a bana.

Idan muka leka fagen siyasa kuwa, ana nan ana ci gaba da fafutukar samun wanda zai dare kujerar shugabancin kasar da kuma ta jam'iyyar ANC.

A shekarar 2019 ne wa'adin Shugaba Jacob Zuma zai kawo karshe, inda kuma ANC za ta zabi sabon jagora a shekarar 2017.

Hukumomi dake bin diddigin al'amura, sun bayyana cewa, rikicin siyasa ma na daya daga cikin abubuwan da ke mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar.

A bangare guda, kotun kundin tsarin mulkin kasar, ta yanke hukuncin cewa, Shugaba Jacob Zuma ya gaza karewa da mutunta kundin tsarin mulkin kasar, saboda ya ki biyan kudaden gyara da ba na tsaro ba, da aka yi a gidansa na kashin kansa. Al'amarin da ya kai ga yunkurin tsige shi daga bangaren 'yan adawa, sai dai, hakarsu ba ta cimma ruwa ba, saboda rinjayen da jam'iyyarsa ke da ita.

Har ila yau, babbar kotun ta kuma bukaci a sabunta tuhumar da ake wa Shugaba Jacob Zuma kan laifuffuka 783 da suka danganci cin hanci da rashawa.

Duk dai a fagen siyasar kasar, wani abu da ke daukar hankali shi ne, yadda a lokuta da dama bangarorin adawa ke kawo tsaiko ga jawaban shugaba Zuma a majalisar dokokin kasar.

Baya ga wannan, bangarorin adawar sun shigar da kara gaban kotu, suna tuhumar gwamnatin kasar da rubuta wasikar neman ficewa daga kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya wato ICC zuwa ga MDD, suna masu cewa, kamata ya yi, a tafka muhawara kan batun kafin yanke shawara.

Sai dai, duk da wadannan dimbin matsaloli, kamfanin tallace-tallacen na Brand South Afrika, ya ce kamar kowace kasa, Afrika ta Kudu ta jure tare da fuskantar matsalolin da suka taso a ciki da wajen kasar.

Da yake gabatar da tsare-tsaren kashe-kashen kudi na matsakaicin zango, ministan kudin kasar Pravin Gordhan, ya ce gwamnati na sa ran samun sama da 1.7% na karuwar tattalin arzikinta a shekarar 2017.

Haka kuma, ya ce a cikin watanni shida na farkon wannan shekarar bangaren yawon bude ido ya samu armashi, domin adadin masu zuwa yawon bude ido daga kasashen waje ya karu da kashi 15.4 cikin dari, inda na masu yawon bude ido na cikin gida ya karu da kashi 23 cikin dari.

Ita ma Cibiyar hakar ma'adanai ta kasar, ta ce za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki, duk dai da nufin habaka tattalin arzikin kasar.

Shugaban cibiyar hakar ma'adanai ta kasar Roger Braxter ya ce, muhimmin abun da bangaren zai sa gaba a shekarar 2017 shi ne, ci gaba da aiki da masu ruwa da tsaki wajen samo mafita ga matsalolin da yake fuskanta tare da tabbatar da dorewar ayyukan bangaren. Yana mai bayyana shi a matsayin jajirceccen bangare da ya shawo kan matsalolin da ya fuskanta a baya.

Shi ma kamfanin Brand South Afrika ta bakin babban manajan bangaren sadarwarsa Manusha Pillai, na da yakinin, hada hannu da masu ruwa da tsaki kamar sashen kasuwanci da zuba jari, da niyyar habaka tattalin azirkin kasar yadda zai fito na fito da sauran kasashe da ake sha'awar zuwa domin zuba jari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China