in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar jakadan Somaliya dake kasar Sin a jami'ar koyon harsunan ta waje ta Beijing
2016-12-29 10:52:56 cri

Jama'a barkannu da warhaka barkanmu da sake kasancewa a cikin wani sabon shirin na Sin da Afrika wanda ke zuwa muku daga sashen Hausa na gidan radiyon kasar Sin wato CRI. To a yau ma Maryam ce ke gabatar muku da shirin, to masu sauraro sai ku gyara zama domin jin yadda shirin zai kasance tare da ni Maryam daga nan sashen Hausa na CRI dake birnin Beijing.

A ranar 7 ga watan Disambar shekarar 2016 ne jakadan Somaliya a kasar Sin Yusuf Hassan Ibrahim, ya gabatar da wani muhimmin jawabi a lokacin da ya ziyarci jami'ar koyon harsunan kasashen waje ta Beijing dake nan kasar Sin wato BFSU.

A cikin jawabin da ya gabatar, jakadan ya tabo muhimman batutuwa game da tarihin dangantakar dake tsakanin Sin da kasar Somaliya. A cewarsa tun a shekarar 1960 ne aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, wato sama da shekaru 50 kenan da suka gabata, kuma Somaliya ce kasa ta farko a gabashin Afrika data fara kulla dangantaka da kasar Sin.

An tambayi jakadan game da wani yunkuri da jama'ar ta BFSU ta ke yi, na kirkiro sashen nazarin yaren kasar Somali, Ambasada Yusuf yace, yana goyon bayan wannan yunkuri, kuma yayi matukar farin ciki da jin wannan kyakkyawan labari.

Wakilin sashen Hausa na gidan radon CRI Ahmad Inuwa Fagam ya tattauna da jakadan game da batun dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Somaliya da kuma sauran batutuwa da suka shafi dangantakar Sin da kasashen Afrika, sai ya fara da tambayarsa ko yaya alakar dake tsakanin kasar ta Somaliya da makwabciyar ta kasar Kenya? Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China