in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya jagoranci shirin raya yankunan yammacin kasar Sin
2016-12-26 10:29:53 cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, zaunannen mamba a hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana firayin ministan kasar Li Keqiang ya jagoranci wani taro, inda aka zartas da shirin raya yankunan dake yammacin kasar Sin, yayin da ake gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13.

Yayin taron, Li Keqiang ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana kokarin samar da wadata ga daukacin al'ummar ta, ciki har da al'ummun dake yankunan yammacin kasar.

Kawo yanzu, an riga an zartas da shirin raya yankunan arewa maso gabashin kasar, da shirin raya yankunan tsakiyar kasa a nan kasar Sin. Ya zuwa ranar 23 ga wannan wata, an gabatar da shirin raya yankunan dake yammancin kasar Sin ga majalisar gudanarwar kasar.

Hakika dai, tun daga shekarar 2000, an fara gabatar da irin wannan shiri, saboda har kullum gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan ci gaban yankunan. A kuma wannan karo, Li Keqiang ya sake jaddada cewa, kasar Sin za ta kara ba da muhimmanci kan aiki. Yana mai cewa, "Yankunan dake yammacin kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin kasar, saboda fadin yankunan ya kai kaso 70 bisa dari na daukacin fadin kasar ta Sin baki daya, kana suna mallakar albarkatun hallitu masu samar da arziki. Ban da haka kuma, yawancin al'ummomin kananan kabilun kasar suna zaune ne a yankunan, wadanda ke da dogon layin iyakar kasa tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. A saboda haka, samar da wadata ga al'ummar yankunan yammancin kasar Sin yana da muhimmanci kwarai, ga yunkurin kasar Sin na cimma burin tabbatar da al'umma mai wadata, da dayantakar kasa, da kuma hada kan kabilu a kasar Sin."

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, idan ana son raya yankunan yammacin kasar, kamata ya yi a kara samar da taimako gare su, kana ya fi muhimmanci a kara gudanar da kwaskwarima da kirkire-kirkire a yankunan, musamman a fannonin saukaka ayyukan hukumomin gwamnati, da kyautata ayyukan ba da hidima, da rage harajin da ake bugawa kamfanonin yankunan da dai sauransu, da haka za a kara shigo da jarin da za a zuba, musamman ma daga wajen 'yan kasuwa masu zaman kansu domin samun ci gaban tattalin arziki a yankunan.

Li Keqiang ya jaddada cewa, kafa kamfanoni a yankunan yammacin kasar Sin yana da babban karfi a asirce, ya ce, "A fannin yin kirkire-kirkire, yankunan yammacin kasar Sin suna iya samu ci gaba kamar yadda yankunan gabashin kasar ke yi, duba da cewa, 'yan kasuwar yankunan yammacin kasar suna gudanar da ciniki kan yanar gizo lami lafiya, kana cikin sauki masu sayayya suna iya sayen kayayyakin gona daga yankunan yammacin kasar. Ana kuma iya jigilar su ga masu saye cikin kwana daya ko biyu kacal. Kaza lika kayayyakin gona na yankunan yammacin kasar Sin, suna samun karbuwa sosai a wajen masu sayayya a fadin kasar ta Sin."

Kawo yanzu an riga an kafa yankunan ciniki marasa shinge guda 11 a fadin kasar Sin, 3 dake cikinsu suna yankunan dake yammacin kasar ne, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan ci gaban yankunan yammacin kasarta.

Game da hakan Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu haka ana kokarin gina wasu muhimman garuruwa na zamani a yankunan, dalilin da ya sa haka shi ne domin jawo hankalin daliban da suka kammala karatu a jami'o'i su rika zama a yankunan yammacin kasar domin yin ayyuka. Li Keqiang yana mai cewa, "Yadda ake gina irin wadannan garuruwan zamani a yankunan yammacin kasar Sin? Abu mafi muhimmanci shi ne a kara mai da hankali kan masana'antu, da aikin gona na zamani, kana kamata ya yi a yi kokarin hana mutane yin kaura daga garururansu zuwa sauran wurare na daban."

Li Keqiang ya jaddada cewa, makasudin raya yankunan yammacin kasar shi ne domin samar da wadata ga al'ummar yankunan, musamman ma domin kyautata zaman rayuwarsu. Yana mai cewa, "Makasudin aikinmu shi ne domin samar da wadata ga al'ummar kasarmu, ciki har da al'ummar dake yankunan yammacin kasar, muna kokarin kyautata sharuddan yankunan a fannonin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da rage talauci da sauransu. Misali, ana kara karbar dalibai daga makarantun yankunan, domin su shiga manyan jami'o'i a manyan biranen kasar domin yin karatu, ta haka za su samu kulawar da jam'iyyar JKS da gwamnatin kasar Sin ke samar musu a yau da kullum."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China