in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kasuwar Sin suna ganin cewa, kara karfin takara da kirkire-kirkire shi ne abu mafi muhimmanci yayin da ake shiga kasuwannin duniya
2016-12-23 13:11:22 cri

A jiya Alhamis a nan birnin Beijing ne, aka gudanar da taron shekara-shekara na kungiyar 'yan kasuwa ta kasa da kasa ta kasar Sin na shekarar 2016, bisa taken "Yadda kamfanofin kasar Sin za su kara himma domin ba da jagoranci a fadin duniya". Shahararrun 'yan kasuwar daga bangaren sana'o'i daban daban kamar masu gina gidajen kwana, da saka kaya, da kera injuna, da sauran sana'o'in dake shafar kimiyya da fasaha na zamani sun hallarta domin yin musanyar ra'ayoyi kan sakamakon da suka samu, inda suka bayyana cewa, kara karfin yin takara da kirkire-kirkire shi ne abu muhimmanci yayin da ake shiga kasuwannin duniya.

A cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, adadin jarin da bai shafi kudi ba da masu zuba jari na kasar Sin suka zuba kai tsaye a kasashen ketare ya zarta kudin Sin RMB biliyan 1000, adadin da ya karu da kaso 55.3 bisa dari idan aka kwatanta da na lokacin bara. Duk da cewa, ana fuskantar matsaloli a fadin duniya, amma kamfanonin kasar Sin suna kokari matuka domin shiga kasuwannin duniya.

Yayin taron wannan shekarar da aka gudanar a jiya, shugaban kungiyar manajoji na rukunin Vanke Wang Shi ya bayyana cewa, rukunin Vanke yana kokarin shiga kasuwannin duniya lami lafiya, saboda ingancin kayayyakin da rukunin ke samarwa, kana har kullum rukunin ya cika alkawarin da ya dauka yayin da yake gudanar da ciniki da sauran kamfanoni. Wang Shi yana mai cewa, "Ina ganin cewa, abu mafi muhimmanci ga kowa ne kamfani shi ne ingancin kayayyakin da yake samarwa ga masu sayayya, kana farashin kayayyakin shi ma yana da muhimanci. A halin da ake ciki yanzu, kayayyakin lantarki da ake amfani da su a cikin gida, ko kayayyakin sadarwa, dukkansu suna fama da goggaya mai tsanani a kasuwannin duniya, a fannin inganci kuwa, kusan babu bambanci tsakanin kayayyakin da ake kerawa a nan kasar Sin da kasashen waje. Ko da yake rukunin Vanke bai dade da zuba jari a kasashen waje ba, amma yana gudanar da aikinsa lami lafiya, saboda rukuninmu yana rike amana, wato yana martaba ka'idojin kwangilolin da aka kulla."

Kamar yadda Wang Shi ya fada, mataimakin shugaban kamfanin sadarwa na ZTE Liu Jian shi ma ya bayyana cewa, kara karfin gogayya yana da muhimmanci kwarai, inda ya yi nuni da cewa, idan har kamfani yana son shiga kasuwannin duniya, wajibi ne ya nuna fiffiko wajen ba da jagoranci ga sauran kamfanonin kasashen waje, a sa'i daya kuma, dole ne ya yi kokarin kara karfin kirkire-kirkire. Liu Jian yana mai cewa, "A fannin kara karfin gogayya, ina ganin cewa, abu mafi muhimmanci shi ne a kara kyautata ingancin kayayyakin da muke samarwa masu sayayya, idan kana son ka samu karbuwa a kasuwannin duniya, wajibi ne ka samarwa masu sayayya kayayyakin da suka zarta na sauran kamfanonin."

Idan har kamfanin ya samar da sabbin kayayyaki masu inganci, amma kayayyakin ba su samu karbuwa a wajen masu sayayya ba, to, wane mataki ke nan za a dauka? Babban manajan kamfanin gina hanya da kadarko na kasar Sin CRBC Lu Shan ya ba da wani misali ga mahalarta taron, inda ya bayyana cewa, kamfaninsa ya taba gamuwa da matsala yayin da yake yin shawarwari da bangarorin da zai yin hadin gwiwa da su domin gina layin dogo tsakanin Hungary da Serbia, saboda kamfanonin kasashen waje suna nuna shakku kan ingancin aikinsa da ma'aunin kasar Sin, amma a karshe dai, kamfanin CRBC ya daidaita lamarin ta hanyar yin hadin gwiwa da sauran kamfanonin kasashen waje. Lu Shan yana mai cewa, "Al'ummomin kasashen Turai suna ganin cewa, yanzu haka akwai jiragen kasa da ke tafiyar da ta zarta kilomita 350 a kowace sa'a a kasar Sin, wannan ya sa suke dauka cewa, kamfanin kasar Sin zai gina layin dogo irin wannan cikin sauki, inda zai samar da jiragen kasa masu saurin tafiya tsakanin kilomita 160 da 200 a kowace awa, amma ba su amince da ingancin aikin kamfanin kasar Sin da ma'aunin kasar Sin ba. Daga baya, mun yi hadin gwiwa da wani shahararren kamfanin Birtaniya da abin ya shafa, domin ya yi musu bayani kan matsayin fasaha na kasar Sin a halin da ake ciki yanzu, a karshe dai mun daidaita lamarin lami lafiya."

Shugaban kungiyar 'yan kusuwa ta kasa da kasa ta kasar Sin Jiang Zengwei yana ganin cewa, kungiyarsa tana taka muhimmiyar rawa wajen shigar da kamfanonin kasar Sin kasuwannin duniya, musamman ma a fannin ba su goyon baya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China