in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Turkiya, Rasha da Iran sun yi shawarwari kan batun Sham kan lokaci
2016-12-21 11:49:20 cri

A ranar Litinin da dare ne, wani dan ta'adda ya harbe har lahira jakadan kasar Rasha dake kasar Turkiya Mr. Andrey Karlov a lokacin da yake halartar bikin baje kolin zane-zane a birnin Ankara na kasar Rasha, gabanin shawarwarin kasashen Rasha da Turkiya da Iran kan batun Sham. Amma duk da haka wannan hari bai kawo illa ga shawarwarin ba. A jiya Talata ne kasashen uku sun kaddamar da shawarwarin a birnin Moscow na kasar Rasha kan lokaci.

Bisa shirin da aka tsara, ya kamata a kaddamar da wannan shawarwari a matakin ministocin kasashen Turkiya da Rasha da Iran a ran 27 ga watan Disamban a birnin Moscow. Amma sabo da ci gaban da aka samu a halin da ake ciki yanzu a birnin Aleppo na kasar Sham, ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Iran suka kudurta kaddamar da wannan shawarwari a jiya Talata a lokacin da suke musayar ra'ayoyi ta waya. Da farko dai a jiyan, an yi shawarwari tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Turkiya da Rasha da Iran, sannan aka yi shawarwari tsakanin ministocin tsaron kasashen uku. Daga baya, an yi wani taron yin shawarwari tsakanin wadannan ministoci 6 tare kan halin da ake ciki yanzu a kasar Sham.

A yayin taron shawarwarin, Mr. Sergey Shoigu, ministan tsaron kasar Rasha ya bayyana cewa, za a ci gaba da daukan matakan yakar ta'addanci. "Ba za mu taba dakatar da aikinmu na dakile ta'addanci a duniya ba, za mu ci gaba da yin wannan aiki. Na yi imani cewa, za mu samu kyakkywan sakamako bisa kokarin da muke yi tare."

Bayan da suka yi tir da ayyukan ta'addancin, sun kuma bayyana batutuwan da za su tattauna, ministocin harkokin wajen kasashen uku da ministocin tsaron kasashen uku bi da bi sun yi taron tattaunawa a asirce. Bayan da suka kammala tarukan nasu, sun kuma fitar da wata sanarwa, kana daga bisani suka shirya wani taron manema labaru, inda mataimakin firaminista kuma ministan harkokin wajen kasar Sham Walid al-Muallem ya ce, wannan ne karo na farko da aka yi shawarwari tsakanin bangarori uku na kasashen Turkiya da Rasha da Iran. A saboda haka wannan wani muhimmin al'amari ne. Ministocin harkokin wajen kasashen uku sun tattauna sosai kan yadda za a bullo da wani tsarin dakatar da bude wuta a yankin Aleppo,da kuma yadda za a iya yi amfani da wannan tsari a sauran yankunan kasar Sham domin kokarin sassauta rikicin jin kai da ake fama da shi a yankin Aleppo, da janye fararen hula daga yanki ba tare da wata matsala ba daga yankin.

Sannan Mr. Sergei Lavrov, ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa, a cikin sanarwar da aka bayar, ministocin harkokin wajen kasashen uku sun jaddada cewa, kasar Sham, kasa ce mai cikakken 'yanci wadda take bin dimokuradiyya. Sergei Lavrov ya bayyana cewa, "Wajibi ne a girmama cikakken 'yancin da dinkuwar kasar Sham. Kowane bangarenmu yana ganin cewa, wajibi ne a kara karfin dakile kungiyar IS a lokacin da ake kokarin bambanta su da dakaru masu adawa da gwamnati mai ci"

Bugu da kari, Mr. Sergei Lavrov ya jaddada cewa, za a ci gaba da kara karfin dakile 'yan ta'adda. A waje daya kuma, za a kara karfin ba da taimakon jin kai ga al'ummomin kasar Sham, kuma za a ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin daidaita batun Sham ta hanyar diflomasiyya.

Ministocin kasashen uku sun kuma bayyana cewa, za su shawo kan gwamnatin Sham mai ci da masu adawa da ita kan yadda za a hanzarta tsara yarjejeniyar yin shawarwari a tsakaninsu. Sannan za a gayyaci kasashen da suke da tasiri a yankin Gabas ta tsakiya ta yadda za su taka rawar a wannan batu. Mr. Sergei Lavrov ya bayyana cewa, "Muna da imani cewa, wannan yarjejeniya za ta yi tasiri ga kokarin daidaita batun Sham a siyasance kamar yadda ya ke kunshe cikin kuduri mai lamba 2254 na kwamitin sulhun MDD. Sannan dukkan ministocin kasashen uku sun yarda da shawarar shugaban kasar Khazakstan ya shirya wani taro a birnin Astana."

Rahotanni na cewa, za a yi taron ganawa tsakanin wakilan gwamnatin Assad ta Sham da na kungiyoyi masu adawa da ita a birnin Astana, babban birnin kasar Khazakstan. Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun amince da wannan shawara a lokacin da suke hira ta waya a makon jiya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China