161221-Wasu-daga-cikin-abubuwan-da-suka-faru-a-nahiyar-Afirka-a-shekarar-2016.m4a
|
Baya ga ire-iren abubuwan da muka ambata a sama da kan faru a cikin kowace shekara, a kan kuma kulla dangantaka ko kai ziyarar sada zumunci tsakanin shugabannin kasashe da nufin kara karfafa dankon zumunci ko huldar cinikayya, al'adu, tattalin arziki da dai sauransu.
A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2016 ne wasu 'yan ta'adda suka kai hari kan wani otel dake birnin Ouagadougou, fadar mulkin Barkina-Faso, inda suka halaka mutane 28, kana wasu 56 kuma suka jikkata.
A shekarar ta 2016 ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar da Gambia da kuma Ghana na baya-bayan nan. Haka kuma a shekarar 2016 da ke shirin karewa ne aka yankewa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre hukuncin daurin rai da rai bisa zarginsa da take hakkin bil-Adama a lokacin da yake mulkin kasar daga shekata ta 1982 zuwa ta 1990.
Muna fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, alheri da karuwar arziki a duniya baki daya a sabuwar shekarar 2017. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)