in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin zuba jarin kasashen Afirka 4 sun iso nan kasar Sin
2016-12-16 13:33:34 cri

A shekaran jiya Laraba ne aka kaddamar da taron kara wa juna sani, tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasashen Afirka guda hudu a birnin Guangzhou dake lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, inda kwararrun hukumomin zuba jari na kasashen Habasha, da Kenya, da Mozambique, da kuma Zambiya, suka yi bayani kan ayyukan zuba jari da muhallin zuba jari na kasashensu, ga kamfanonin kasar Sin da yawansu ya kai sama da 200. Kana kai tsaye 'yan kasawar Sin da na kasashen Afirka sun yi musanyar ra'ayoyi masu zurfi.

Tun bayan da aka kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2000, fahimtar juna a fannin siyasa tsakanin sassan biyu na kara zurfafuwa a kai a kai, kana huldar tattalin arziki da ciniki tsakaninsu ita ma ta samu ci gaba cikin sauri. Abu mafi faranta ran mutane shi ne, a cikin shekaru 7 da suka gabata, kasar Sin ta kasance kasa mafi girma wajen ciniki a nahiyar Afirka, yayin da nahiyar ta Afirka ita ma ta kasance kasuwa mafi muhimmanci ta kasar Sin a ketare.

Yayin taron kara wa juna sani, mataimakin shugaban sashen sa kaimi kan ciniki da zuba jari na hukumar sa kaimi kan ciniki ta kasar Sin Zhu Lingyan ta bayyana cewa, "Har kullum kasashen Habasha da Kenya da Mozambique da Zambiya da kasar Sin, na samun ci gaba tare bisa tushen moriyar juna, kuma wadannan kasashe hudu suna da fiffiko wajen kasuwa, kana suna da karfin samun bunkasuwa a asirce, a saboda haka sun kasance muhimmiyar kasuwa ta kasar Sin a ketare."

Habasha kasa ce a Afirka mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki, kuma ta samu jarin waje kaso 60 bisa dari daga kasar Sin. Shugaban sashen sa kaimi kan zuba jari na hukumar zuba jari ta kasar Aschalew Tadesse Mesheso ya yi mana bayani cewa, kasar ta Habasha ta tsara shirin raya kasa, kuma tana sa ran cewa, za ta kasance cibiyar kera injuna a Afirka nan da shekarar 2025. Domin cimma wannan burin, kasar Habasha tana bukatar kara shigo da jarin waje. Tadesse yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, kayan sawa da tufafi su ne ayyuka mafiya muhimmanci a kasarmu, dalilin da ya sa haka shi ne muna shuka auduga da dama, kuma muna da 'yan kwadago matasa da dama. Kana kasarmu babbar kasa ce a fannin aikin gona, shi ya sa muka fi mai da hankali kan aikin gyara kayayyakin aikin gona, muna fatan za mu kara samun riba daga hakan. Ban da wannan kuma, muna kokarin raya masana'antu, musamman ma fannin samar da karfe, da injuna, da kayayyakin gine-gine da sauransu. A saboda haka muna maraba da kamfanonin da abin ya shafa su zo kasarmu domin zuba jari. Kazaclika, za mu kara kafa manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, kamar su hanyar mota, da layin dogo, da jiragen kasa, da kuma tashar ruwa."

Tadesse shi ma ya yi bayani kan matakan da kasarsa ta dauka wajen jawo hankalin masu zuba jari. Misali za a mayar da jarin da za a zuba ga masu zuba jari, kuma kamfanonin suna iya hayar ma'aikata 'yan asalin kasashensu a kasar ta Habasha, domin su yi aiki a cikin kamfanoninsu, za a kuma rage harajin kwastan, da soke harajin da za a buga musu da dai sauransu. Tadesse ya ce, za a aiwatar da wadannan manufofi a wasu cibiyoyin masana'antun kasar har da tsawon shekaru goma.

Daga baya kwararru a fanin zuba jari da suka zo daga Kenya da Zambiya da kuma Mozambique, su ma sun yi bayani kan muhallin zuba jari da damammakin zuba jari dake kasashensu.

Yayin taron, mataimakin shugaban asusun raya Sin da Afirka Wang Yong ya bayyana cewa, tun bayan da aka kafa asusun raya Sin da Afirka kafin shekaru 9 da suka gabata, bisa jimilla adadin ayyukan da asusun ya zuba jari kan su ya riga ya kai 88, kuma al'ummomin kasashen Afirka 36 sama da mutum miliyan 1 sun samu moriya daga hakan. Wadannan ayyuka suna shafar fannonin manyan kayayyakin more rayuwar al'umma, da gyara kayayyaki, da samar da makamashi, da ma'adinai da kuma aikin gona. Wang Yong yana mai cewa, "A cikin shekaru 9 da suka gabata, asusun raya Sin da Afirka ya zuba jarin da yawan sa ya kai dalar Amurka biliyan 4 kan ayyuka 88. An yi hasashen cewa, kamfanonin kasar Sin za su kara zuba jari kan wadannan ayyuka. Kana bankunan kasar Sin za su samar da rancen kudi, kuma mai yiwuwa ne adadin jarinsu zai kai dalar Amurka biliyan 17. Shi ya sa ina iya cewa, mun taka muhummiyar rawa a fannin."

Wani jami'in cibiyar cinikin kasa da kasa ta MDD Ashish Shah ya bayyana cewa, jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen Afirka ya sassauta matsalar talaucin da suke fuskantar, kuma ya kyautata ingancin zaman rayuwar al'ummar nahiyar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China