in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kasuwancin Sin ya jaddada cewa, kasarsa za ta kiyaye hakkinta na halal
2016-12-13 10:51:27 cri

Ya zuwa ranar 11 ga watan Disambar bana, kasar Sin ta riga ta shafe shekaru 15 a kungiyar cinikayya ta duniya, bisa abubuwan da aka tanada a cikin digo na 15 na "yarjejeniya game da shigar da kasar Sin kungiyar cinikayya ta duniya", an ce, a hukunce kasashe mambobin kungiyar za su daina aiwatar da manufar farashi ga kasar Sin, wato nuna kiyayya ga sayar da kayayyaki masu yawan gaske cikin farashi mai araha a wannan rana, amma kawo yanzu, wasu kasashe mambobin kungiyar kamar su Amurka da Japan da kuma wasu kasashen Turai, ba su da niyyar cika alkawarinsu. A saboda haka, jiya Litinin ministan kasuwancin kasar Sin Gao Hucheng ya rubuta wani rahoto, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta nace ga kiyaye moriya da hakkinta na halal, kuma mai yiwuwa za ta dauki matakai domin cimma wannan buri.  

Bisa abubuwan da aka tanada a cikin digo na 15 na "yarjejeniya game da shigar da kasar Sin kungiyar cinikayya ta duniya", an ce, a hukunce kasashe mambobin kungiyar za su daina aiwatar da manufar farashi ga kasar Sin, wato nuna kiyayya ga sayar da kayayyaki masu yawan gaske cikin farashi mai araha a ranar 11 ga watan Disambar bana, daga nan, kasashe mambobin kungiyar ba za su iya yin amfani da farashi iri na kasa ta uku da suka zaba yayin da suke gudanar da bincike kan kayayyaki masu yawan gaske da kasar Sin ta sayar da su cikin farashi mai araha ba, amma wasu kasashe ba sa son cika wannan alkawari na su.

Game da wannan, ministan kasuwancin kasar Sin Gao Hucheng ya rubuta wani rahoto a jaridar "People's Daily", inda ya yi suka kan wadannan kasashe saboda a cikin ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya, babu irin wadannan abubuwan da aka tanada. A hakika ma dai, ka'idojin kungiyar sun riga sun kasance kashi guda a cikin dokokin kasashen duniya, cewa wajibi ne daukacin kasashe mambobin kungiyar cinikayya ta duniya su bi ka'idojin. Idan wasu kasashe sun ki yin hakan, to, kasar Sin za ta dauki matakai domin kiyaye hakkinta na halal. Hakan shi ma ya nuna cewa, kasar Sin za ta yi kokari tare da yawancin kasashe mambobin kungiyar cinikayya ta duniya, wajen gudanar da tsarin cinikayya dake tsakanin bangarori da dama yadda ya kamata.

Kwararriya dake aiki a cibiyar nazarin huldar zamani tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin Chen Fengying tana ganin cewa, yanzu haka wasu jami'an hukumomin gwamnatin kasar Sin da dama sun jaddada cewa, kasar Sin za ta dauki matakai domin kiyaye hakkinta na halal, hakan ya nuna cewa, kasar Sin za ta yi amfani da ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya domin kiyaye moriya da hakkinta. Chen Fengying tana mai cewa, "Da farko dai, ko daga ra'ayin da kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya nuna a gaban jama'a, ko ma ta jawabin da ministan kasuwancin kasar Sin ya rubuta a jarida, ana iya gano cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin cinikayya dake tsakanin bangarori da dama. Wajibi ne ko wace kasa mambar kungiyar ta cika alkawarin da ta dauka, idan wasu kasashe ba za su cika alkawarinsu ba, to, kasar Sin za ta kai kara bisa ka'idojin kungiyar. Kana kungiyar cinikayya ta duniya tana da tsarinta na warware sabani. Ban da wannan kuma, a halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a cinikayyar duniya, shi ya sa, za a mai da hankali kan ra'ayin na kasar Sin. "

Mataimakin shugaban kungiyar nazarin kungiyar cinikayya ta duniya a kasar Sin Xue Rongjiu yana ganin cewa, idan wasu kasashe ba za su cika alkawarinsu ba, to kasar Sin tana iya daukan wasu matakai kamar haka, ya ce, "Ina ganin cewa, kasar Sin tana iya daukar matakai a fannoni da dama, alal misali, kai kara ga kungiyar cinikayya ta duniya domin ta daidaita batun da tsarinta wajen warware sabani, idan wasu kasashe sun ci gaba da aiwatar da manufar farashi kan kasar Sin, kasar Sin za ta iya aiwatar da manufar da ta yi kama da wannan a kan su, idan haka ta auku, ana iya fuskantar yakin ciniki, wanda ka iya kawo illa ga sassan biyu."

An ce, tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya kafin shekaru 15 da suka gabata, gaba daya kasashe mambobin kungiyar sama da 80 sun riga sun daina aiwatar da manufar farashi irin na kasa ta uku kan kasar Sin. Kana wasu masanan tattalin arziki na kasashen Amurka da Turai da Japan su ma sun bayyana cewa, ya kamata a daina aiwatar da manufar kafin cika shekaru 15 da shigar kasar Sin kungiyar cinikayya ta duniya.

Mataimakin shugaban ofishin nazarin harkokin kasashen Turai na cibiyar nazarin huldar zamani tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin Wang Shuo na ganin cewa, kasar Sin tana fuskantar damammaki da kalubale, kuma ya kamata kasar Sin ta yi amfani da damammakin ta kamar yadda ta yi kafin shekaru 15 da suka gabata, domin samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya. Yana mai cewa, "Yanzu kasar Sin tana fama da tasirin da rikicin kudi da basussuka ke kawo mata, amma idan ta yi amfani da damammakin ta, to, za ta samu ci gaba bisa tushen moriyar juna tare da sauran kasashen duniya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China