161214-Ziyarar-aikin-da-abokan-aikinmu-suka-kai-birnin-Quanzhou-dake-lardin-Fujian-na-kasar-Sin.m4a
|
Baya ga wannan masallaci mai dadadden tarihi, sun kuma ziyarci wasu daga cikin wuraren addinan Buddah da na mabiya darikar Katolika, inda suka ga wasu muhimman gine gine masu dadadden tarihi a wannan birnin na Quanzhou.
Kasancewar wannan ziyara ta shafi wurare na musamman, sun kuma ziyarci wani kanti sayar da kofi na musamman wanda wata mace Basiniya tare da hadin gwiwar mai gidanta suke gudanar da harkokin kasuwanci tare a wannan shago.
Sannan kuma sun ziyarci sauran wurare da suka hada da wuraren sarrafa 'ya'yan itatuwa ko kuma kayan marmari da ake hada abinci na musamman. A taikace dai ziyara ce mai matukar armashi kuma mai cike da tarihi.
Mun tattauna da Ahmed Fagam game da wannan ziyara a cikin wannan shiri, da fatan za ku kasance tare da mu. (Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)