in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana kara kokarin kwato kudaden da masu cin hanci suka ajiye a kasashen ketare
2016-12-09 13:16:19 cri

Ranar 9 ga watan Disamba, rana ce da MDD ta kebe ta yaki da cin hanci da rashawa a duniya, a ko wace shekara MDD ta kan yi kira ga kasashen duniya da su gudanar da ayyuka domin yada manufa game da wannan batu a wannan rana. A cikin shekarar bana da za ta shude, ba ma kawai kasar Sin ta yi kokarin yaki da cin hanci da rashawa a cikin gidan kasar ba, har ma ta samu babban sakamako wajen karbon kudaden da mutane masu cin hanci da rashawa suka ajiye a kasashen ketare, tare kuma da bukatar gwamnatocin kasashen da su mayar da wadannan kudadaen da masu aikata laifuffuka suka boye zuwa gida kasar Sin.

Ranar 16 ga watan Nuwamban bana, mai aikata laifin dake kan gaba a cikin takardar sunayen mutane 100 da suka gudu zuwa kasashen waje tare da kudaden da suka samu ta hanyar cin hanci da rashawa da hukumar shari'ar kasar Sin ta sanya domin kame su a kasashen waje, tare da karbo kudaden da suka ajiye a waje Yang Xiuzhu ta koma nan kasar Sin da kanta domin karbar hukuncin da za a yanke mata. A filin saukar jiragen saman kasa da kasa na birnin Beijing, ma'aikatan hukumar shari'ar lardin Zhejiang suka sanar da umurnin kame ta, daga nan Yang Xiuzhu ta kammala gudunta a kasashe shida a cikin shekaru 13 da suka gabata.

Kwanaki hudu kafin wannan, wato ranar 12 ga watan Nuwamban bana, mai aikata laifi na 5 dake cikin takardar sunayen mutane 100 da suka gudu zuwa kasashen waje tare da kudaden da suka samu ta hanyar cin hanci da rashawa da hukumar shari'ar kasar Sin ta sanya domin kame su a kasashen waje, tare da karbo kudaden da suka ajiye a waje Yan Yongming shi ma ya dawo nan kasar Sin da kansa daga kasar New Zealand bayan gudun da ya yi a kasar a cikin shekaru 15 da suka gabata, kuma ya mayar da kudade da yawa da ya samu ta hanyar cin hanci da rashawa ga gwamnatin kasar Sin, ana iya cewa, kasar Sin ta samu sakamako mai faranta ran mutane a fannin a cikin shekarar da muke ciki.

Kwanakin baya ba da dadewa ba, darektan ofishin kula da aikin na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban hukumar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ta kwamitin ladaftarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Liu Jianchao ya yi bayani ga manema labarai game da sakamakon da kasar Sin ta samu a wannan fannin a shekarar bana, inda ya bayyana cewa, "Ya zuwa watan Nuwambar bana, gaba daya kasar Sin ta kama masu aikata laifuffukan cin hanci da rashawa da yawansu ya kai 908 daga kasashe da shiyyoyi sama da 70, a cikinsu kuwa, ma'aikatan hukomomin gwamnatin kasar Sin suk kai 122, kana adadin kudaden da aka karbo daga wajensu ya kai RMB yuan biliyan 2 da miliyan 312, kuma 19 daga cikinsu suna cikin takardar sunayen mutane 100 da suka gudu zuwa kasashen waje tare da kudaden da suka samu ta hanyar cin hanci da rashawa da hukumar shari'ar kasar Sin ta sanya domin kame su a kasashen waje, tare da karbo kudaden da suka ajiye a waje. Tun bayan da aka fara gudanar da aikin a shekarar 2014, gaba daya an kama masu aikata laifuffuka 2442 a kasashen waje, adadin kudaden da suka mayar ya kai RMB yuan biliyan 8 da miliyan 542."

Liu Jianchao ya kara da cewa, tsarin kama masu cin hanci da rashawa a kasashen waje da karbo kudaden da suka ajiye a ketare na kasar Sin yana kyautata a kai a kai, yanzu dai ana gudanar da aikin bisa hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama, kamar na siyasa, da diplomasiya, da dokoki, da ra'ayin bainal jama'a, da sauransu. Liu Jinchao yana mai cewa, "Misali, an sanar da sunayen masu aikata laifi ga jama'a a fadin duniya, a saboda haka al'ummar kasar Sin da na kasashen waje suna iya sanar da 'yan sanda idan suka gano su ko tarar da wurin boyensu, ban da wannan kuma, muna kokarin sanar da masu aikata laifuffuka cewa, ya fi dacewa su koma gida kasar Sin da kansu, idan suka ki karbar hukuncin da za a yanke musu, to, hukuncin zai kara tsanani."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, yayin da kasar Sin take kokarin yaki da cin hanci da rashawa, sai dai a sa'i daya kuma, tana kokarin yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya, har ta gabatar da wasu shawarwari a jere a fannin. Yayin taron kolin G20 da aka gudanar a birnin Hangzhou a watan Satumbar bana, shugabannin kasashe daban daban suka zartas da "babbar ka'idar yaki da cin hanci da rashawa ta rukunin G20", da "shirin aikin yaki da cin hanci da rashawa tsakanin shekarar 2017 da 2018" a karkashin kokarin da kasar Sin ta yi, inda aka bukaci kasashen da su samar da wajibabbun sharuda ga aikin. Liu Jianchao ya bayyana cewa, "Sau da dama kasar Sin takan gabatar da tunaninta a fannin yaki da cin hanci da rashawa a gaban shugabannin kasashen duniya, musamman ma wajen kama masu cin hanci da rashawa a kasashen waje da karbo kudaden da suka ajiye a ketare, bayan kokarin da ta yi, tunanin ya samu karbuwa daga wajen sauran kasashen duniya, ana iya cewa, Sin ta ba da babbar gudummuwa a fannin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China