in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar dogon Tazara da gadar Nyerere alamu ne na zumunci tsakanin Sin da Tanzaniya
2016-12-07 12:22:26 cri

Idan aka ambata kasar Tanzaniya, to, nan take za a tuna da hanyar dogon Tazara wato hanyar dogo ce da aka gina a Tanzaniya bisa tallafin kasar Sin domin hada birnin Dares Salam na kasar da garin Kapiri Mposhi na kasar Zambiya, yanzu dai gadar Nyerere da kamfanin kasar Sin ya gina kan teku tana amfanawa al'ummar kasar ta Tanzaniya sosai, ita ma ta kasance alama ce ta sada zumuncin dake tsakanin Sin da Tanzaniya.

Kafin shekaru sama da 40 da suka gabata, kwararru da injiniyoyi da dama na kasar Sin sun tafi Tanzaniya mai nisa sosai dake nahiyar Afirka, domin gina layin dogo a kasar, ya zuwa ranar 14 ga watan Yulin shekarar 1976, a hukumance ne wannan layin dogo ta Tazara da take hada birnin Dares Salam na Tanzaniya da garin Kapiri Mposhi na kasar Zambiya ta fara aiki, hanyar tana da tsawon kilomita 1860.5, a wancan lokaci ta taka muhimmiyar rawa wajen sufuri a yankin gabashin Afirka da kuma kudu maso tsakiyar nahiyar, har ta sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki a yankunan.

A halin da ake ciki yanzu, gadar Nyerere da rukunin CRCEG na kasar Sin wato rukunin gina layin dogo na kasar Sin ya gina a Tanzaniya, ita ma tana bada gudumawa a kasar kamar yadda layin dogon Tazara ta yi. A watan Afililun bana, wannan gadar da aka gina kan teku ta hanyar yin amfani da fasahar zamani ta fara aiki a hukumance, yanzu dai ta riga ta kasance alamar da ta fi shahara a yankin gabashin Afirka.

Gadar Nyerere ta taimaka matuka kan zaman rayuwar yau da kullum na al'ummar wuraren, mazaunin birnin Dares Salam Eli Thea ya yi mana bayani cewa, "Kafin wannan gadar ta fara aiki, mu kan shafe sa'o'i sama da biyu domin tashi daga nan zuwa wancan gabar teku, saboda dole ne mu shiga jirgin ruwa, ko tafiya da kafa, amma yanzu, tun bayan da aka fara amfani da gadar, muna iya ketare teku mu isa daya gabar cikin mintoci talatin, gaskiya muna jin dadi, kana, gadar Nyerere ta kasance wurin shakatawa a birninmu, masu yawon bude ido da dama su kan zo wurin domin daukan hotuna, har wasu matasa su kan zo nan domin daukan hotunan bikin aure, wato amarya da ango su kan sa tufafin bikin aure su dauki hotuna a nan tare da gadar."

Wani abokinsa shi ma ya bayyana cewa, wannan gada tana da muhimmnaci matuka ga mazauna birnin, musamman ma ga mutanen da suka kamu da cututtuka, saboda wajibi ne su je asibiti cikin gajeren lokaci.

Kafin a kammala aikin gina gadar, ana shan ayyuka da dama, ya zuwa watan Fabrairun shekarar 2012, sai aka fara gina wannan gada.

Babban manajan rukunin gina layin dogo na kasar Sin reshensa a yankin gabashin Afirka wanda ke sauke nauyin gina gadar Nyerere a Tanzaniya Xie Zhixiang, ya yi mana bayani cewa, idan a kasar Sin, gina wata gada iri na gadar Nyerere, to, babu matsala ko kadan, amma a Tanzaniya, ba haka yake ba, an yi kokari matuka.

Xie Zhixiang ya kara da cewa, kamfanonin kasar Sin sun zo Tanzaniya, ba ma kawai sun zo ne tare da aminci ba, har ma suna kokarin sada zumunta dake tsakaninsu da al'ummar kasar ta Tanzaniya. Yana mai cewa, "Ya zuwa bana, kamfaninmu ya riga ya gudanar da aikinsa a kasar Tazaniya har tsawon shekaru 40, a cikin wadannan shekarun, ko wace shekara mu kan yi hayar mazaunan wuraren kasar domin su yi aiki a kamfaninmu kusan dubu 5, adadin da ya kai kashi 90 cikin dari dake cikin daukacin ma'aikatan kamfaninmu a kasar ta Tanzaniya."

Gadar Nyerere ta kara kyautata kayayyakin more rayuwar al'ummar kasar ta Tanzaniya, kana ta samar da taimako ga mazaunan yankunan kasar wajen samun fasahohin zamani, musamman ma wajen fasahar gina gada.

Injiniya a fannin gina gada na Tanzaniya Lamar ya gaya mana cewa, "Gadar Nyerere gada ce ta farko da aka gina ta hanyar fasahar zamani a yankin gabashin Afirka, wato aka rataya gada da layi cikin sararin sama, gaskiya ta ba mu mamaki, a baya ban taba ganin irinta da idona ba, sai cikin bidiyo, amma yanzu na shiga aikin gida ta, wannan karo ne na farko a gare ni, nayi farin ciki kwarai da gaske, ni ma na koyi abubuwa da dama daga wajen."

Ban da hanyar dogon Tazara da gadar Nyerere, yanzu tunanin gudanar da hada-hadar kudi da harkokin kamfanoni na kasar Sin da ma'aunin fasahohin kasar Sin suna samun karbuwa daga wajen al'ummar kasar ta Tanzaniya a kai a kai, ko shakka babu duk wadannan za su taimaka wajen samun ci gaban tattalin arziki a kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China