in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kyautata manufar diplomasiya domin daga matsayinta a duniya
2016-12-05 11:11:57 cri

A shekarar 2016 da muke ciki, kasar Sin ta samu babban sakamako a dandalin diplomasiya na kasa da kasa, har ya jawo hankalin jama'ar kasashen duniya, ana iya cewa, kasar tana kokarin kyautata manufofin da take dauka kan harkokin waje domin daga matsayinta a duniya.

A shekarar bana da muke ciki, ana gudanar da shirin "ziri daya da hanya daya" lami lafiya, wato kasar Sin ta riga ta daddale yarjejeniyar hadin gwiwa kan shirin da kasashen duniya da kuma kungiyoyin kasa da kasa sama da 40, kana kasar Sin ta gabatar da shirinta game da ci gaban tattalin arziki a taron kolin G20 da aka gudanar a birnin Hangzhou na jihar Zhejiang yayin da kasashen duniya ke fama da matsala a wannan fannin, ban da haka kuma kasar Sin ta sa kaimi kan aikin zartas da "sanarwar Lima game da kafa yankin ciniki maras shinge a Asiya da tekun Pasifik" a gun kwarya kwaryar taron shugabannin kasashen mambobin kungiyar APEC da aka kira kwanakin baya ba da dadewa ba, gaskiya kasar Sin tana kokarin kyautata manufofin diplomasiya domin kara daga matsayinta a duniya.

Kamar yadda kuka sani, yanayin siyasar kasashen duniya ya samu manyan sauye-sauye a bana, tattalin arzikin kasashen duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, kasar Birtaniya ta fice daga kungiyar kasashen Turai EU ba zato ba tsammani, halin siyasar da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki ya kara tsanani, har wasu kasashen duniya ba su so su samu ci gaba tare da sauran kasashe daban daban a fadin duniya ba, game da wannan, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, "A halin da ake ciki yanzu, yanayin duniya na samun manyan sauye-sauye, hakan ya kawo hali maras tabbas da tangarda ga duniyarmu, duk da cewa, kasashen duniya suna fuskantar sabbin kalubale, amma a sa'i daya kuma, sun samu sabbin damammakin samun ci gaba, a saboda haka, abu mafi muhimmnanci shi ne su yi amfani da wadannan damammaki, tare kuma da tinkarar matsalolin dake gabansu."

To, a cikin wannan shekarar da za ta gabata, ta yaya kasar Sin ta yi kokari domin gudanar da aikin diplomasiyarta yadda ya kamata? Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako a fannoni da dama, musamman ma wajen ba da jagoranci kan aikin yin kwaskwarima kan tsarin tafiyar da harkokin duniya, da kiyaye zaman lafiya a shiyya shiyya, da kiyaye huldar dake tsakaninta da wasu manyan kasashen duniya kamar su Amurka da Rasha da sauransu, da kiyaye ikon mallakarta a tekun Nanhai, da gudanar da shirin "ziri daya da hanya daya" da sauransu. Wang Yi yana mai cewa, "Ba ma kawai kasar Sin ta kiyaye muhalli mai inganci ga ci gabanta ba, har ma ta daga matsayinta a fadin duniya, ko shakka babu kasar Sin ta samu babban sakamako a fannin kyautata manufofin diplomasiyarta masu tsarin musamman na kasar Sin."

A bayyane ne taron kolin G20 da aka gudana a birnin Hangzhou na jihar Zhejiang dake kudancin kasar Sin ya fi jawo hankalin jama'ar kasashen duniya, shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin tabbatar da hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasashen duniya. Ana ganin cewa, taron kolin G20 na Hangzhou ya sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Masanin tattalin arzikin duniya dake aiki a cibiyar nazarin huldar kasashen duniya ta kasar Sin Chen Fengying tana mai cewa, "Yayin taron kolin G20 na Hangzhou, mun gabatar da wani shiri game da yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, kana mun gabatar da cewa, a halin da ake ciki yanzu, abubuwa mafi muhimamnci yayin da ake kokarin raya tattalin arziki su ne ciniki da zuba jari, shi ya sa wajibi a kara mai da hankali kan fannonin."

Yayin taron, karo na farko ne aka samu sakamako a fannonin 29, kuma karo na farko ne aka mayar da tunanin kirkire-kirkire da batun samun dauwamammen ci gaba a matsayin abu mafi muhimmanci na taron, kana karo na farko ne aka tsara tsarin zuba jari dake tsakanin bangarori da dama a fadin duniya, kazalika, karo na farko aka bayar da sanarwar shugaba kan batun sauyin yanayi.

Shekarar 2016 za ta gabata, a cikin shekarar 2017 da za mu shiga, kasar Sin za ta ci gaba da sanya kokari domin kara taka rawa a kan dandalin diplomasiyar kasashen duniya, bari mu sa ido mu gani.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China