in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin Ban-kwana da Mamane Ada
2016-12-11 12:04:17 cri

A ranar 11 ga watan Disamban shekarar 2016 ne abokin aikinmu Mamame Ada daga Jamhuriyar Nijar zai ajiye aiki, bayan ya shafe shekaru bakwai yana aiki a sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin (CRI) wato daga watan Disamban shekarar 2009 zuwa watan Disamban shekarar 2016.

A iya tsawon shekaru bakwai din da ya shafe yana aiki a sashen Hausa, Mamane Ada ya gabatar da labarai da rahotanni da sauran shirye-shirye, kamar shirin Allah daya gari banban.

Mamane Ada mutum ne mai sha'awar al'adun gargajiya, wannan ya sa ya ke ziyartar wuraren kade-kade da raye-rayen Sinawa a duk inda ya samu kansa a sassan kasar Sin.

Sai ku kasance da mu a shirinmu na "Gani ya kori ji na musamman" na ban kwana da muka tattauna da shi. Daukacin ma'aikatan sashen Hausa na yi masa fatan alheri. (Ada,Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China