in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya mika ta'aziyya ga shugabannin kasashen Brazil da Bolivia
2016-11-30 20:57:48 cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Brazil Michel Temer da na Bolivia Evo Morales, dangane da jirgin saman nan da ya yi hadari a Colombia, inda mutane 71 suka mutu, ciki har da 'yan wasan wata tawagar kwallon kafan kasar Brazil.

A jiya Talata ne jirgin saman da aka yi shatarsa dauke da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chapecoense, ya fado a yankin kasar Colombia, inda ya halaka mutane 71 da ke cikinsa, galibi 'yan wasan kungiyar da ma'aikatan jirgin saman na kasar Bolivia guda 6. Mutane 6 ne dai suka tsira a hadarin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China