in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta dauki mataki don tabbatar da dokar hana muzgunawa iyali
2016-11-25 13:06:37 cri

Ranar 25 ga watan Nuwamba, rana ce da aka ware don hana muzgunawa iyali a duniya, tun bayan da aka fitar da dokar hana muzgunawa iyali a nan kasar Sin, sai hukumomin gwamnatin da abin ya shafa na wurare daban daban a fadin kasar suka dauki matakai a jere a fannonin gabatar da kara cikin lokaci, da yin gargadi ga masu aikata laifin, da sanarwar ba da kariya ga iyalan da suke fuskantar muzgunawa da dai sauransu domin tabbatar da wannan dokar.

An samu labari cewa, tun bayan da aka fitar da dokar hana muzgunawa iyali a kasar Sin a watan Maris na shekarar da muke ciki, kawo yanzu gaba daya jihohi da birane 17 a kasar sun riga sun fidda tsari da kuma takardun da suka shafi aiwatar da dokar hana muzgunawa iyali, har adadinsu ya zarta dari daya. Kana hukumomin kula da kwaciyar hankalin jama'a a kasar suna tallafawa wadanda suka gabatar da bukatar neman taimako a fannin cikin lokaci, a sa'i daya kuma, sun fitar da wasu dabaru domin bayar da gargadi ga masu aikata laifukan muzgunawa iyali.

Yau Jumma'a mataimakin shugaban hukumar kula da kwanciyar hankalin jama'a ta birnin Nanjing na lardin Jiangsu dake kudancin kasar Sin Jiang Ping, ya halarci wani taron tattaunawa kan batun hana muzgunawa iyali, inda ya yi nuni da cewa, tabbatar da tsarin yin gargadi ga masu aikata laifin zai taimaka wajen hana tsanantawar laifin muzgunawa iyali, haka kuma zai ba da gudumuwa a fannin kiyaye tsaron lafiyar jikin al'ummar kasar, kana zai kyautata huldar dake tsakanin mambobin iyali, tare kuma da kara sa kaimi kan zaman jituwa da zaman karko a zamantakewar al'ummar kasar ta Sin. Jiang Ping ya ba da misali cewa, "Alal misali, a birninmu na Nanjing, wata mata a unguwar Jiangning da ake kiranta da suna Cui, ta kan yi cacar baki da mijinta mai suna Wang, har mijn nata ya kan buge ta, a saboda haka Cui ta sha gabatar da bukatar neman taimako wajen 'yan sanda a lokuta da dama tun daga bara har zuwa yanzu, daga baya, 'yan sanda sun shiga tsakani, kuma sun warware matsalar, amma a ranar 16 ga watan Maris na bana, Cui da mijinta Wang sun sake yin cacar baki, Wang ya sake bugun matarsa Cui, nan take 'yan sanda suka kai dauki gidan nasu ba tare da bata lokaci ba, sun hana Wang sake aikata wannan laifin, kuma sun ba shi takardar gargadi, tare kuma da koyar da shi dokar da abin ya shafa. Bayan ya karbi takardar gargadin da 'yan sanda suka mika masa, sai Wang ya ji tsoro, ya nemi gafara daga wajen matarsa Cui, kuma ya yi alkawari cewa, ba zai sake bugunta ba a nan gaba. Daga baya, 'yan sanda suka sake shiga gidan nasu domin yin bincike, abu mai faranta ran mutane shi ne, huldar dake tsakanin Cui da Wang ta kyautata, yanzu suna jin dadin zaman rayuwa yadda ya kamata."

Umarnin ba da kariya ga tsaron lafiyar jikin al'umma shi ma ya taimaka wajen hana muzgunawa iyali, bisa dokar hana muzgunawa iyali, an tanada cewa, idan an gamu da matsalar muzgunawa iyali, ko ya yi hasashe zai gamu da matsalar a cikin gida, to yana iya neman kariya don samun tsaron lafiyarsa, kana idan wanda zai aikata laifin ya ki karbar umarnin, shi ma zai fara aiki nan da nan, idan wanda ya gabatar da bukatar neman samun wannan umarnin ya samu umarnin, to zai iya hana a aikata laifin muzgunawa iyali, har zai iya kore mutum dake zargin zai aikata laifi daga gidansu, idan akwai bukata, 'yan sanda za su dauki matakai domin kara tabbatar da tsaronsa.

Mataimakin shugaban ofishin nazarin dokar aure da iyali na cibiyar nazarin dokokin kasar Sin Li Mingshun, yana ganin cewa, "Muhimmin amfanin umarnin ba da kariya ga tsaron lafiyar jikin al'umma shi ne, hana aukuwar muzgunawa iyali da kuma hana sake aukuwar laifin, idan ana fuskantar matsalar, kamata ya yi a gabatar da bukatar neman samun wannan umurnin, ta haka za'a iya gujewa aukuwar muzgunawa iyali."

Mataimakiyar shugaban kungiyar mata ta kasar Sin Song Xiuyan, ta bayyana cewa, kungiyar matan kasar Sin za ta ci gaba da yada manufa game da dokar hana muzgunawa iyali, domin kara kyautata huldar dake tsakanin mambobin iyali. Song Xiuyan tana mai cewa, "Idan ana son tabbatar da dokar hana muzgunawa iyali a kasar Sin, kamata ya yi a kara mai da hankali kan ayyukan da abin ya shafa, misali kyautata aikin karbar korafe korafen da matan da suke shan wahalar muzgunawar iyali suka gabatar, tare kuma da warware matsalar a kan lokaci, da samar da taimako ga matan dake cikin mawuyancin halin muzgunawa iyali, da budewa layukan waya domin amsa tambayoyin matan dake fuskantar matsalar muzgunawa iyali, da kuma samar da taimako ga mata ta yanar gizo, kana a kara samar da tallafi ga mata da yara wadanda ke bukatar taimako, ka zalika, a kara ba da muhimmanci kan al'amuran dake da nasaba da muzgunawa iyali, ta haka ne za a iya cimma burin kiyaye ikon halal na mata da yara yadda ya kamata." (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China