161123-Muhimmancin-taron-COP22-ga-matsalar-sauyin-yanayin-duniya.m4a
|
Bugu da kari, a ranar 7 ga watan na Nuwamba ne aka fara taron kwanaki 11 na kasashen da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a birnin Marrakech na kasar Morocco. Yanzu haka dai kasashe kimanin 100 ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya.
A watan Disamban shekarar 2015 ne aka amince da yarjejeniyar a birnin Paris na kasar Faransa. Kana a watan Oktoban shekarar 2016 da muke ciki, kasashe 96 da kungiyar tarayyar Turai (EU) suka sanya hannu a kanta, daga bisani kuma yarjejeniyar ta fara aiki a ranar 4 ga watan Nuwamban wannan shekara.
Masana dai na nuna cewa, duk irin sakamakon da za a samu ko aka samu a yayin manyan tarukan tinkarar sauyain yanayi na duniya za su yi tasiri matuka ga 'yancin kowane mutum game da neman samun ci gaba a duniyarmu.
Masu fashin baki na ganin cewa, batun tinkarar sauyin yanayin duniya, ba batu ne na siyasa ba kawai, wannan al'amari ne na tattalin arziki. Don haka, muddin ana bukatar yarjejeniyar ta taka rawar da ta dace a kokarin da ake yi na magance matsalar sauyin yanayin duniyar da muke ciki, wajibi ne kasashe da kungiyoyin da abin ya shafa su cika alkawarin da suka dauka daga dukkan fannoni. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)