161122-ranar-Afirka-ta-Kudu-BNDS-maryam.m4a
|
Kwanan baya, daliban makarantar Beijing National Day sun shirya bikin ranar Afirka ta Kudu domin kara sani da fahimtarsu kan al'adun kasa ta Afirka ta Kudu, inda suka shirya taruka da dama domin kara ilimantar da sauran daliban wannan makaranta abubuwan da suka shafi kasa ta Afirka ta Kudu kamar kabilu, tufafi, sun kuma shirya wani bikin dandana abincin kasar.
Malama Marya Yang da malam Saminu Alhassan sun halarci bikin ranar Afirka ta Kudu da daliban suka yi, inda suka tattauna da yin gasa tare da daliban makarantar kan harkokin kasar Afirka ta Kudu, har ma na kasashen Afirka baki daya, haka kuma, malam Saminu ya koya musu harshen Hausa bisa gayyatar da daliban makarantar suka yi masa, ga yadda daliban suka koyon harshen Hausa, da kuma karin bayanin da muka kawo muku dangane da wannan biki.