in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana kokarin samun dauwamemmen ci gaba ta hanyar kyautata makamashi
2016-11-18 12:51:25 cri

Jiya Alhamis zaunannen mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, firayin ministan kasar, kana darektan kwamitin kula da makamashi na kasar Li Keqiang, ya jagoranci wani taron kwamitin makamashi na kasa, inda aka zartas da "shirin raya kasa na shekaru biyar biyar a fannin ci gaban makamashi", wanda aka tsara bisa shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na kasar Sin, kuma aka gabatar da jadawalin ayyukan da suka shafi hakan.

Yayin taron, kwamitin kwaskwarima da raya kasa na kasar Sin, da hukumar kula da makamashi ta kasar sun bayar da rahotanni kan sakamakon da suka samu, inda Li Keqiang ya bayyana cewa, makamashi yana da muhimmancin gaske wajen raya kasa. Kuma a halin da ake ciki yanzu, tsarin makamashin kasashen duniya yana fuskantar manyan sauye-sauye, yayin da kasashen duniya ke kokarin kyautata fasahohin amfani da makamashi, a saboda haka, bisa matsayinta na babbar kasa a fannin samar da makamashi da kuma yin amfani da makamashi, kamata ya yi kasar Sin ta mai da hankali kan damammakin dake gabanta, ta yi amfani da sabon tunanin samun ci gaba, kana ta yi kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen duniya, domin kara kyautata tsarin makamashi yadda ya kamata.

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, idan ana son kyautata aikin samar da makamashi a kasar Sin, ya fi kyau a kara ba da muhimmanci kan aikin samar da makamashi ta hanyar amfani da kwal da fasahar zamani, kana ya kamata a kara samar da makamashi ta hanyar yin amfani da makamashi mai tsabta kamar su ruwa, da iska, da hasken rana da sauransu. Ban da wannan kuma, a sa kaimi kan aikin raya makamashin nukiliya, wanda ta haka ne za a kyautata tsarin makamashi a kasar Sin.

A fannin amfani da makamashi kuwa, Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu haka gwamnatin kasar Sin na kokarin daukan matakai daban daban, misali a fannin tattalin arziki, da na dokoki, domin aiwatar da manufofin tsimin makamashi, da kuma rage fitar da gurbatacciyar iska, musamman ma a fannin masana'antu da gine-gine da sufuri. Li Keqiang ya kara da cewa, idan ana son cimma wannan buri, ya kamata a kara kyautata hanyar amfani da makamashi, tare kuma da kara kyautata al'adar zaman rayuwar al'ummar kasar. A halin da ake ciki yanzu, abu mafi muhimmanci shi ne a gudanar da aikin samar da dumamar iska ga gidajen kwana na mazaunen biranen dake arewacin kasar Sin a lokacin sanyi, haka kuma a yi kokarin rage fitar da gurbatacciyar iska.

Li Keqiang ya jaddada cewa, abubuwan da suka fi muhimmanci yayin da ake sa kaimi kan aikin samun dauwamammen ci gaban makamashi a kasar Sin su ne, kara hanzarta saurin kirkire-kirkiren fasahohi, da kuma kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki a kasar. Ya ce ya zama wajibi hukumomin gwamnatin kasar Sin su kara karfafa zuciyar ma'aikatan kamfanonin samar da makamashi, da hukumomin nazarin makamashin, domin su yi kirkire-kirkire kan fasahohin amfani da makamashi. Kana a yi kwaskwarima kan kasuwar makamashi ta hanyar saukaka manufofin gwamnati, da kyautata hidimomin da ake samarwa a fannin makamashi. Kazalika, ya dace a shigo da jarin 'yan kasuwa cikin kasuwar makamashi, yayin da ake zurfafa gyare-gyare kan kamfanonin makamashi na gwamnatin kasar. A karshe, za a cimma burin kafa wani tsarin kasuwar makamashi mai adalci a kasar ta Sin.

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, idan ana son tabbatar da tsaron makamashi a kasar, to, dole ne a yi la'akari da yanayin cikin gida da na kasashen ketare baki daya, wato ba ma kawai mai da hankali kan tsarin makamashi a cikin gida na kasar ba, har ma da kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, da haka ne za a kafa wani tsarin samar da makamashi mai inganci.

Ana iya cewa, ya fi kyau a ci gaba da gudanar da hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da wasu kasashen dake samar da makamashi irin na gargajiya, kana a kyautata tsarin cinikin makamashi, wato a yi amfani da shirin "ziri daya da hanyar" domin kara habaka hadin gwiwar makamashi tsakanin kasa da kasa. Yanzu haka kasar Sin tana kokarin shiga aikin kyautata hanyar yin amfani da makamashi tare da sauran kasashen duniya, a sa'i daya kuma, tana ba da gudumawarta wajen kafa wani tsarin makamashin duniya mai adalci a fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China