161114-maman-kawo-hasken-rana-lubabatu.m4a
|
A kididdigar da aka yi, an ce, yanzu haka a nan kasar Sin, yawan masu shan miyagun kwayoyi sun zarce miliyan 14, wanda kuma ke ci gaba da karuwa. Baya ga haka, matsalar miyagun kwayoyi na janyo asarori da suka kai kimanin kudin Sin yuan biliyan 500 a fannin tattalin arziki. Har wa yau, kisan kai da kuma laifuffuka a sanadin shan miyagun kwayoyi ma na faruwa a kai a kai.
yau za mu kawo muku wani labari mai armashi sosai game da wasu mata da ke lardin Guizhou a kudu maso yammacin kasar Sin, wadanda suke taimakawa masu shan miyagun kwayoyi wajen dakatar da shan su.