161116-Ranar-matasan-Afirka-ta-kungiyar-AU.m4a
|
Albarkacin wannan rana, matasa a sassa daban-daban na Afirka sun shirya bukukuwa, da taruka da shirye-shiryen rediyo da talabijin da sauransu, da nufin karfafawa juna gwiwa ta hanyar amfani da yawansu a cikin al'umma don sa kaimi ga ci gaban nahiyar.
A wannan shekara, matasa a sassan nahiyar sun shirya tattaunawa a kafofin sadarwa na zamani ta hanyar amfani da maudu'in "Afirkan da muke son gani" don shata nahiyar da suke fatan gani mai cike da zaman lafiya da wadata.
Yanzu haka kungiyar AU ta fara sanya mata da matasa a cikin dukkan ayyukan ci gaba da take gudanarwa, ta yadda za a rika damawa da su a dukkan harkokin kungiyar.
Bikin na wannan shekara zai mayar da hankali ne wajen ganin an kara damawa da matasa a ayyukan raya kasa, da kara Ilimantar da su a harkokin zuba jari da kara musayar al'adu da fahimtar juna tsakanin matasan nahiyar.
Sauran fannonin sun hada da hadin gwiwa tsakanin matasa da sassa masu zaman kansu ta yadda za a kara samar da guraben ayyukan yi, da fasahohin raya sana'o'i ta yadda za a inganta rayuwar matasa.
Masana na ganin cewa, kasancewar matasa a matsayinsu na manyan gobe, kamata ya yi gwamnatocin kasashe a dukkan matakai su fito da shirye-shirye don magance zaman kashe wando, yayin da a hannu guda su ma matasan ya kamata su tashi tsaye don bayar da tasu gudummawar ta yadda haka za ta cimma ruwa. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)