161108-ginawar-tashar-samar-wutar-lantarki-a-Equatorial-Guinea-maryam.m4a
|
Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 46 da kafa dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Equatorial Guinea. Hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da bunkasa a fannoni daban daban cikin yanayi mai kyau, har ma ana iya ganin harkokin kasar Sin da ayyuka ko ina a kasar Equatorial Guinea, sabo da kamfanonin kasar Sin da dama suna aikin gina ababen more rayuwa, da gine-gine daban daban, ciki har da kamfanin gina kayayyakin samar da wutar lantarki da karfin ruwa na kasar Sin, wanda ya gina ya kuma gudanar da harkokin babbar tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa ta Djibloho, wadda ta samar da wutar lantarki ga gidaje masu dimbin yawa a kasar Equatorial Guinea. Ga kuma cikakken rahoton da malam Saminu ya hada mana kan wannan batu: