in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana fatan kasa da kasa za su iya gane ainihin burin 'yan aware na Hong Kong
2016-11-07 20:08:00 cri

A yau Litinin da safe, zaunennen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta zartas da wani bayani dangane da tanadi na 104 na dokokin Hong Kong, wanda ya jawo hankalin wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa. A game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, harkar Hong Kong harkar gida ce ta kasar Sin, don haka, bai kamata a tsoma baki a ciki ba, Sin tana fatan kuma a gane ainihin burin 'yan aware na Hong Kong.

A taron manema labarai da aka kira a wannan rana, kakakin ya jaddada cewa, Hong Kong yankin musamman ne na kasar Sin, wanda ke karkashin shugabancin gwamnatin kasar. Yadda 'yan aware na Hong Kong ke kokarin balle yankin daga kasar ta Sin ya saba wa dokoki da kuma ra'ayin al'umma, hakan ba ma kawai ya lalata mulkin kan kasar Sin da tsaronta, haka kuma ya lalata moriyar yankin Hong Kong da ma moriyar kasa da kasa da ke yankin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China