in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS ta fitar da sabuwar ka'idar gudanar da harkokinta
2016-11-03 13:31:21 cri

A jiya Laraba ne aka fitar da "wasu ka'idoji game da harkokin siyasa a cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS, a karkashin sabon yanayin da ake ciki yanzu", da "ka'idar sa ido kan 'yan jam'iyyar JKS" a hukunce a nan birnin Beijing. Ka'idojin da aka amincewa a yayin cikakken taro na shida na kwamitin tsakiyar JKS na 18 da aka kammala a kwanakin baya ba da dadewa ba.

Makasudin da aka fitar da wadannan takardun biyu shi ne domin kara karfafa da kuma kyautata harkokin siyasa a cikin jam'iyyar JKS a karkashin sabon yanayin da ake ciki, tare kuma da kara karfafa aikin sa ido kan 'yan jam'iyyar. Masanan da abin ya shafa suna ganin cewa, matakin da jam'iyyar JKS ta dauka ya alamanta cewa, kasar Sin ta riga ta fara gudanar da harkokin jam'iyyar mulkin kasar wato JKS bisa ka'idojin da aka tsara.

Bisa takarda mai taken "wasu ka'idoji game da harkokin siyasa a cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS a karkashin sabon yanayin da ake ciki yanzu" wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya fitar jiya, aka kuma gabatar da bukatu a fannoni sha biyu, wadanda suke kumshe da nacewa ga tunanin jam'iyyar, da nacewa ka'idar tushen jam'iyyar, da nacewa kiyaye ikon mulkin kwamitin tsakiyar jam'iyyar JKS, da nacewa ka'idar siyasar jam'iyyar, da tabbatar da ikon demokuradiyar 'yan jam'iyyar, da kara karfafa kayyade da kuma sa ido kan ikon jami'an jam'iyyar, da dai sauransu.

Takardar game de "ka'idar sa ido kan 'yan jam'iyyar JKS" tana kuwa kumshe da abubuwan da suke shafar yadda za a raba ayyukan sa ido ga hukumomin jam'iyyar JKS bisa mataki daban daban.

Shehun malamin dake aiki a kwalejin horas da jami'an hukumomin gwamnatin kasar Sin Zhu Lijia yana ganin cewa, wadannan takardun biyu da aka fitar suna da babbar ma'ana, saboda sun alamanta cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta shiga wani sabon babi, yayin da take kokarin yaki da cin hanci da rashawa; wato yanzu haka tana gudanar da harkokin ta bisa ka'idojin da aka tsara yadda ya kamata. Ana iya cewa, takardun biyu za su ba da babbar gudumawa kan aikin kyautata yanayin da jam'iyyar JKS ke ciki, kana za su taka muhimmiyar rawa wajen kara kyautata yanayin zaman takewar al'ummar kasar Sin. Zhu Lijia yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta shiga wani sabon mataki na kwaskwarima da kuma samun ci gaban tattalin arziki, kana ta gamu da wahalhalun da ba a taba ganin irinsu ba a tarihi, a karkashin irin wannan hali ne, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ita ma ta gamu da matsaloli. Alal misali, matsalar cin hanci da rashawa, to ko yaya za a daidaita wadannan matsalolin? Yanzu haka an fitar da takardun biyu, mun hakakke cewa, za su taimaka wajen kyautata yanayin da ake ciki yanzu, za kuma su ba da gudumawa wajen kago wani muhalli na samun ci gaba na gari a kasar ta Sin, da haka ne kuma za a cimma burin tabbatar da wadata a kasar yadda ya kamata."

Mataimakin darektan cibiyar yin nazari kan aikin gwamnati ta jami'ar Beijing Zhuang Deshui yana ganin cewa, wadannan takardun biyu za su warware sabbin matsalolin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta gamu a sabon halin da ake ciki. Ya ce, "Yanzu yanayin gudanar da harkokin jam'iyyar JKS ya sauya, tun bayan da aka gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar JKS karo na 18, mun tarar da wasu sabbin matsalolin da muke fama da su, wadanda ba mu iya daidaita su bisa ka'idojin da aka tsara a baya ba, don haka ake kokarin tsara sabbin ka'idoji domin warware sabbin matsalolin."

Masanan da abin ya shafa suna ganin cewa, wadannan takardun biyu suna da nasaba da ka'idoji da aka tsara a baya, kuma sun yi amfani mutuka wajen inganta sakamakon da jam'iyyar JKS ta samu a cikin 'yan shekarun da suka gabata, musamman ma bayan da aka gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar JKS karo na 18 a shekarar 2012, kuma wasu akwai sabbin matakan da za a dauka wadanda za su fi jawo hankalin jama'a. Zhuang Deshui ya bayyana cewa, "Alal misali, ka'idar sa idon da aka tsara, yanzu dai an bayyana cewa, za a sa ido kan jami'an jam'iyyar, musamman ma manyan jami'an gwamnatin kasar, kuma an bukaci manyan jami'an da su zamo abun misali na gari ga sauran jami'ai, su kuma gudanar da aikinsu bisa ka'ida yadda ya kamata, kana an bukace su da su sa ido kan abokan aiki ko iyalai dake kusa da su, domin kara kyautata aikin sa ido da ake yi. Ban da wannan kuma, takardun sun bukaci daukacin 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da su shiga aikin sa ido."

An ce, kafin a fitar da wadannan takardun biyu, an nemi jin ra'ayoyin wakilan bangarori daban daban domin neman jin ta bakin su, da shawarwari daga wajen su, an kuma zanta da wakilai da ba na 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China