161109-JKS-ta-fito-da-kaidojin-tafiyar-da-harkokin-jamiyya-Sanusi.m4a
|
Bayan taron, an kuma zartas da muhimman takardu biyu wadanda za su ba da jagoranci kan yadda za a tafiyar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, takarda ta farko ita ce, "wasu ka'idoji game da harkokin siyasa a cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a sabon halin da ake ciki yanzu", ta biyu kuma ita ce, "wasu ka'idoji game da sa ido kan halin da 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suke ciki". Kana an fitar da tsarin gudanar da harkokin JKS a hukumance wato za a kafa kwamitin tsakiyar JKS a karkashin jagorancin babban sakataren JKS Xi Jinping.
Haka kuma an yi kira ga daukacin 'yan jam'iyyar da su hada kai domin kara kyautata ka'idojin jam'iyyar, tare kuma da kara zage damtse da dukkanin Sinawa, ta yadda za a cimma burin bude sabon babi yayin da ake gina sha'anin gurguzu mai tsarin musamman na kasar Sin.
Masana na cewa, idan har ana son kara kyautata ka'idojin JKS, wajibi ne a gudanar da harkokin siyasa na jam'iyyar bisa ka'idojin da aka tsara.
haka kuma, idan ana son kara kyautata harkokin siyasar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, dole ne a kara sa ido kan manyan shugabannin jam'iyyar, musamman ma mambobin kwamitin tsakiyar JKS, da hukumar siyasar kwamitin tsakiyar JKS, da kuma zaunannen kwamitin hukumar siyasar kwamitin tsakiyar JKS. A baya, sabbin shugabannin kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun tsara ka'idoji guda takwas tun bayan da suka fara gudanar da mulki a kasar ta Sin domin samar da muhallin siyasa na gari a kasar.
Masu sharhi sun bayyana cewa, wannan taron da aka gudanar yana da babbar ma'ana, saboda a yayin wannan taron ne aka ba da umurnin kara kyautata ka'idojin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ana iya cewa, taron ya samar da tabbaci ga Sinawa a fannonin tunani da tsari yayin da ake kara hada kai karkashin jagorancin shugaban kasar Sin, sannan ya alamanta cewa, an bude wani sabon babi na gina babban sha'ani a kasar Sin a karkashin jagorancin JKS. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)