161102-Kasar-Sin-ta-tsara-zamanantar-da-aikin-gona-nan-da-shekarar-2020-Sanusi.m4a
|
Manufar tsarin ita ce samar da isasshen abinci, da tabbatar da ingancin kayayyakin abincin da ake samarwa a fadin kasar ta Sin, tare da karfafa gogayyar kasar ta fuskar samar da abinci a duniya nan da shekara ta 2020.
Har wa yau tsarin zai baiwa mazauna yankunan karkarar kasar Sin damar gudanar da ingantacciyar rayuwa daidai wa daida, za kuma a yi amfani da tsarin wajen kafa cibiyoyin gwajin ayyukan gona na zamani a sassa daban daban na kasar.
Kaza lika, tsarin zai taimaka wajen inganta ayyukan kirkire-kirkire, da na gudanarwa, tare da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, baya ga batun bude kofofin ci gaba ga manoma.
Masu sharhi na bayyana wannan mataki a matsayin babban ci gaba a kokarin da mahukuntan kasar Sin ke yi na inganta rayuwar al'ummarta daga dukkan fannoni, kasancewar "Noma shi ne tushen arziki" (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)