in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Filayen jiragen sama kadan ne suke amsa ka'idojin tsaro a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika
2016-11-01 10:45:02 cri
Kashi 7 cikin 100 ne kawai na filayen jiragen sama suke amsa ka'idojin tsaro a kasashe takwas na yammaci da tsakiyar Afrika, in ji kungiyar sufurin jiragen saman fararen hula ta kasa da kasa (OACI) reshen yammaci da tsakiyar Afrika (WACAF), a yayin wani zaman taron na takardar shaidar jiragen sama a yankin, dake gudana daga ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba a birnin Lome.

Wakilan sufurin jiragen saman fararen hula na Burkina Faso, Kamaru, Cote d'Ivoire, Nijar, Najeriya, Senegal, Mali da Gambiya sun taru a Lome domin ingiza shirin shiyya bisa koyi da misalin kasashen Togo, Ghana, Mauritaniya da Cap Vert da suke cikin ka'idojin.

Haduwar Lome zata taimakawa mahalartan dasu saba tare da cigaban matakan da kasashe masu takadar shaida ta filayen jiragen samansu suke aiwatarwa da kuma rage adadin haduran jiragen sama a cikin mahalartan kasashen takawas.

Zabin Togo wajen karbar bakuncin wannan zaman taro na bayyana cewa itace kasa daya daga cikin kasashen da suka sami takardar shaida akalla daya daga cikin filayen jiragen samansu na kasa da kasa, a cewar masu shirya wannan haduwa.

Don haka, a yayin wannan zaman taro Togo zata raba kwarewarta tare da sauran kasashe. Idan aka san muhimmancin bada kariya da tsaron sufurin jiragen sama, takadar shaida ta wani filin jirgin sama ta zama wata bukata ta dole, in ji kanal Dokissime Gnama Latta, darekta janar hukumar sufurin jiragen saman fararen hula ta kasar Togo (ANAC).

Afrika na wakiltar kashi 4 cikin 100 na harkokin sufurin jiragen sama amma kuma kashi 35 cikin 100 na hadura, wannan yayi yawa sosai. Dole a rage wadannan hadura. A cikin shiyyar ECOWAS, kasar Togo ita ce kasa ta farko cikin kasasshe uku da suka sami shaidar filin jiragen samansu. Ya zama wajibi mu sanya niyya tare kuma Togo ta sami zarafin raba kwarewarta, in ji mista Gnama Latta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China