in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daliban Equatorial Guinea suna sha'awar koyon Sinanci
2016-10-31 11:12:19 cri

A halin da ake ciki yanzu, hadin gwiwa a fannoni daban daban da musanya tsakanin kasar Sin da kasar Equatorial Guinea da ke yankin yamma maso tsakiyar nahiyar Afirka, na ci gaba da karuwa, a kan ga 'yan kasar Equatorial Guinea dake aiki a filayen saukar jiragen sama, ko ma'aikatan kwastan na kasar na gaida ko yin hira da Sinawa wadanda suka sauka a kasar su da harshen Sinanci.

Yanzu haka an kafa kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius a jami'ar kasar ta Equatorial Guinea, a saboda haka daliban kasar masu dimbin yawa ke sha'awar koyon Sinanci.

A ranar 25 ga watan Janairun shekarar bana wato shekarar 2016 da muke ciki ne a hukunce, aka kaddamar da kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius a jami'ar kasar Equatorial Guinea dake birnin Malabo, fadar mulkin kasar. Wannan kwalejin Confucius ita ce ta farko a kasar ta Equatorial Guinea, wadda jami'ar kasar Equatorial Guinea da kwalejin harsunan waje ta lardin Zhejiang na kasar Sin suka kafa cikin hadin gwiwa. Kuma kawo yanzu, adadin daliban da suka yi rajista a kwalejin domin koyon Sinanci na karuwa cikin sauri.

Shugaba na farko na bangaren kasar Sin a kwalejin Li Zhitao, ya yi mana bayani cewa, tun bayan da aka kafa kwalejin, ta samu ci gaba cikin sauri, a watan Fabrairun bana, bisa mataki na farko an karbi dalibai 62, yanzu haka kuma ana shirin kara karbar dalibai. Li Zhitao ya bayyana cewa, "Ana iya cewa, dalibai masu dimbin yawa suna da sha'awar koyon Sinanci, a ajin mu da aka kafa a birnin Malabo dake tsibirin Bioko, mun samu dalibai 180, a ajinmu dake birnin Bata kuwa, mun samu dalibai 170, haka kuma adadin daliban da muka samu yana karuwa, kila adadin zai kai 400 a nan gaba. Muna farin ciki kwarai ganin daliban da suke koyon Sinanci na yawaita a wannan karamar kasar ta Equatorial Guinea."

Shugaban kwalejin na bangaren Equatirial Guinea Fernando Panades Garcia ya kammala karatunsa ne a jami'ar horas da malamai ta Nanjing ta lardin Jiangsu na kasar Sin, yana iya yin magana da Sinanci ne sosai, yana ganin cewa, kafa kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius a kasar ta Equatorial Guinea zai taimakawa 'yan kasar da su kara fahimtar abubuwan dake da nasaba da kasar Sin. Yana mai cewa, "Mutanen kasar Equatorial Guinea ba su san abubuwan dake shafar kasar Sin sosai ba, yanzu da aka kafa kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius a kasar, ana iya cewa, hakan zai taimakawa 'yan kasar wajen kara fahimtar kasar Sin, musamman ma al'adun kasar Sin. Ina ganin cewa, lamarin yana da babbar ma'ana, saboda daliban kasarmu sun nuna sha'awa kan Sinanci."

Jesus Alfonso Abeso Nguema Mbang, dalibi ne a jami'ar kasar Equatorial Guinea, yanzu haka yana koyon Sinanci a kwalejin Confucius, ya bayyana mana cewa, "Ina da sha'awar koyon Sinanci, tun bayan da na fara koyon Sinanci a kwalejin Confucius, na fara iya hira da Sinawa, nan gaba kuma zan yi kokarin neman samun damar koyon Sinanci a kasar Sin. Duk da cewa koyon Sinanci yana da wahala, amma na samu ci gaba saboda kokarin da nake yi, zan ci gaba da kwazo wajen koyon Sinanci."

Shugaban kwalejin Li Zhitao ya yi mana bayani cewa, a kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius da aka kafa a kasar ta Equatorial Guinea, ban da Sinanci, ana kuma koyar da dalibai rera wakokin Sinanci, da wasan Kongfu, da wasan Taiji, da wasan darar chess na kasar Sin. Li Zhitao yana ganin cewa, baya ga samar da wani dandali na yada Sinanci da al'adun kasar Sin da kwalejin Confucius take yi, tana kuma samar da wata gada ga kasashen biyu wato Sin da Equatorial Guinea, wajen yin musanyar al'adu tsakaninsu, yana mai cewa, "Muna son yin amfani da wannan dandali da kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius ta samar mana, domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kwalejin harsunan waje dake lardin Zhejiang na kasar Sin, da jami'ar kasar Equatorial Guinea. Alal misali, dalibai ko malamai na kwalejin harsunan waje dake lardin Zhejiang na kasar Sin, wadanda ke koyon harshen Spaniya, za su iyar samun damar zuwa nan kasar ta Equatorial Guinea domin koyon harshen Spaniya, yayin da dalibai ko malamai na jami'ar kasar ta Equatorial Guinea kuma su ma za su iyar samun damar karatu a kasar Sin. Har wa yau sassan biyu za su samu damar fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin ba da ilmi yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China