in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ga yadda dokokin tattalin arziki da cinikayya za su kiyaye hadin gwiwar Sin da Afirka
2016-11-02 15:31:55 cri

Kwanan baya, an yi taron karawa juna sani na kasa da kasa game da kalubalolin da ake fuskanta a fannin dokoki a yayin da ake zuba jari da harkokin tattalin arziki da cinikayya. Hukumar tsara dokoki ta kasar Sin ce ta jagoranci wannan taro na kwanaki biyu, wanda ya fara a ranar 20 ga watan Oktoba, yayin da hukumar nazarin dokokin kungiyar kasuwanci ta duniya ta WTO da cibiyar tsara dokoki ta kasar Sin suka taimaka mata wajen shirya taron.

Wakilai kinamin dari biyu daga hukumomin tsara dokoki da na kasuwanci wadanda suka zo daga kasashen Asiya, Afirka da kuma Turai ne suka halarci wannan taro, inda suka tattauna game da kalubalolin da ake fuskanta a fannin dokoki a yayin da ake zuba jari a harkokin tattalin arziki da cinikayya da kuma yadda za a warware matsalolin da abin ya shafa.

A yayin bikin bude taron, mataimakin shugaban hukumar tsara dokokin ta kasar Sin Chen Jiping ya bayyana cewa, rashin fahimtar dokoki, al'adun jama'a da kuma harsuna na kasashen Afirka, sune suke haddasa matsaloli ga kamfanonin kasar Sin dake son zuba jari a wajen, shi ya sa, ya kamata a kara yin mu'amala da kuma yin nazari kan dokoki da al'adun kasashen da abin ya shafa, ta yadda za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasashen Afirka yadda ya kamata.

Dangane da wannan lamarin, na tattaunawa da babban mai shari'a a kotun tarayyar Nijeriya Ibrahim Auta, ga kuma yadda tattaunawarmu ta kasance:

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China