161026-Muhimmancin-sanya-kudin-kasar-Sin-RMB-cikin-tsarin-SDR-Sanusi.m4a
|
Asusun na IMF ya ce wannan wani babban ci gaba ne tun bayan da aka sanya kudin Euro cikin tsarin SDR, kuma shigar da kudin kasar Sin cikin wannan tsari, abu mai matukar muhimmanci ga tsarin, asusun IMF, kasar Sin da kuma tsarin hada-hadar kudi na duniya.
Shigar da kudin RMB ya sabunta tsarin SDR na asusun IMF, wanda ya sa tsarin SDR ya kara samun wakilcin kudaden duniya da tattalin arzikin duniya, kana ya shaida ci gaban da aka samu dangane da kwaskwarimar da aka yi wa tsarin kudin Sin, da musayar kudade da hada-hadar kudi, kana kasashen duniya su ma sun nuna amincewa ga wannan ci gaba.
Asusun IMF ya bullo da tsarin SDR ne a shekarar 1969 don taimakawa kasashe membobin kungiyar wajen adana kudade. Shigar da kudin RMB a cikin tsarin SDR ya shaida canjan tsarin tattalin arzikin duniya, da samun ikon fada a ji a tsakanin wasu kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki a tsarin hada-hadar kudi na duniya, kana ya mayar da amsa bukatun da kasashen duniya suka gabatar tun farko na yin kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudi na duniya.
Masu sharhi na cewa,wannan mataki alheri ne ga kasashe masu tasowa,baya ga muhimmiyar rawa da RMB zai taka wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)