161019-Mahukuntan-Sin-sun-kara-bullo-da-matakan-kawar-da-Talauci-Sanusi.m4a
|
Takardar ta bayyana cewa, gwamnati za ta shigar da kudade masu yawa ga yankunan da suka fi fama da talauci domin dakile fatara, da samar da ci gaba mai dorewa.
Takardar mai lakabin "Ci gaban Sin a fannin yaki da fatara da kare hakkin bil'adama", ta nuna cewa, kudin da aka tanada domin wannan aiki, za su kai kudin kasar Sin RMB biliyan 189.84, kimanin dalar Amurka biliyan 28.17. Za kuma a kashe su ne tsakanin shekarun 2016 zuwa 2020.
Ya zuwa karshen shekarar bara, akwai matalauta da suka kai mutane miliyan 55.75 a cikin kasar Sin, wadanda kuma ake fatan fitar da su daga wannan yanayi nan da shekara ta 2020.
Cikin shekaru 30 da suka gabata, tun fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje, da sauye sauye ga tattalin arzikin kasar, mahukuntan kasar sun cimma nasarar ceto kimanin mutane miliyan 700 daga kangin talauci.
Rahoton MDD game da kudurorin ci gaban muradun karni na bara, ya nuna cewa, adadin wadanda ke cikin matsanancin kangin talauci a kasar Sin ya sauya, daga kashi 61 bisa dari a shekarar 1990 zuwa kashi 4.2 cikin 100 a shekarar 2014. A hannu guda kuma adadin matalauta da kasar ta ceto daga wannan yanayi, ya kai kasshi 70 bisa dari na jimillar adadin a dukkanin fadin duniya.
Masu fashin baki na cewa, sabon matakin da mahukuntan kasar suka kuduri aiwatarwa ya samu yabo matuka, matakin da ke nuna aniyar kasar ta inganta rayuwar al'ummominta. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)