in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran raya hadin gwiwar yawon shakatawa a tsakanin Sin da Afirka
2016-10-19 09:00:46 cri

A kwanakin baya ne aka bude taron tsibiran yawon shakatawa na kasa da kasa na shekarar 2016 a tsibirin Zhoushan na lardin Zhejiang dake nan kasar Sin. Taken taron na kwanaki biyu shi ne, amfani da sabuwar hanyar siliki ta ruwa wajen raya tsibirai da tekuna ba tare da gurbata muhalli ba.

Abokin aikinmu Ibrahim Yaya ya halarci taron na tsibirin Zhoushan, ya kuma yi tattaunawa da Isma'ila Jayeoba Adekunle, kwamishinan harkokin cinikayya da yawon shakatawa na jihar Osun, kuma jami'in tuntuba a harkar cinikayya a jihar Osun ta tarayyar Najeriya.

Cikin shirinmu na wannan mako, mun gayyato malam Ibrahim, inda ya tattauna kan wannan taron da aka yi da kuma ziyararsa a tsibirin Zhoushan, sa'an nan, mun kawo masu sauraronmu tattaunawar dake tsakanin malam Ibrahim da malam Isma'ila na jihar Osun.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China