in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi liyafar taya murnar bikin kasa a nan kasar Sin
2016-10-01 13:28:44 cri

A daren jiya Jumma'a, majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya liyafar ban girma, don taya murnar cika shekaru 67 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, inda wasu shugabannin kasar, ciki har da shugaban kasa Xi Jinping, da firaminista Li Keqiang da dai sauransu, suka taya murnar wannan gagarumin biki tare da wakilai na cikin gida da na ketare, wadanda yawansu ya wuce 1200.

A yayin bikin, firaminista Li ya ce, tun shekaru 67 da suka wuce, musamman ma bayan da aka soma yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta shugabanci jama'ar kasar, don cimma burin juya matsayin kasar daga kawar da talauci da karfafa karfin kasa zuwa babbar kasa ta biyu a duniya ta fuskar tattalin arziki.

Firaminista Li ya kara da cewa, samun wadata a cikin kasa babban tushe ne wajen kara samar da gajiya ga jama'a. Saboda haka, kamata ya yi a tsaya kan raya tattalin arzikin kasa, a yayin da ake kokarin tabbatar da samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri, a sa'i daya kuma a yi kokarin hana hadarurruka daban daban. Kana a karfafa karfin kasa na yin kirkire-kirkire da na yin takara, da inganta matsayin kasa na samun dauwamammen ci gaba, ta yadda za a ciyar da tattalin arzikin kasa gaba.

A cewar firaministan, ya kamata a yi kokarin biyan bukatun jama'a, da daukar matakan da suka dace, don sanya jama'ar kasar su iya samun nasara a fannin samar da guraben aiki da kafa sana'a, tare kuma da kara samun kudin shiga. Kana a kara ba da tabbaci ga jama'ar kasar, ciki har da ciyar da tsofaffi, ganin likita, da samun gidajen kwana. Bayan haka kuma, a kara ingancin zaman rayuwar jama'a ta fuskokin kiyaye muhallin halittu, da abinci da dai sauransu. Haka zalika a kara karfin kawar da talauci, domin sanya mutane masu fama da talauci su iya zama cikin wadata tun da wuri.

Firaminista Li ya kuma kara da cewa, ya kamata a gudanar da harkokin kasa bisa dokoki, da kara kiyayen ikon mallakar tattalin arziki daban daban, kana da shigar da dukkan bangarorin dake shafar kasuwanci cikin takara yadda ya kamata, da karfafa adalci wajen samar da hidimomin jama'a, domin sanya dukkan jama'ar kasar samun cin gajiya daga nasarorin da aka samu sakamakon yin kwaskwarima da ci gaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China