in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wajibi ne a kiyaye ikon MDD, in ji Li Keqiang a yayin babban taron MDD
2016-09-22 10:51:10 cri

Jiya Laraba da safe, agogon wurin, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya yi jawabi a yayin da ake yin babbar muhawara a gun babban taron MDD karo na 71 da ake gudanarwa a birnin New York na kasar Amurka, inda ya jaddada cewa, wajibi ne a kiyaye tsarin kasa da kasa na yanzu dake karkashin jagorancin MDD da ka'idar huldar kasa da kasa da aka tsara bisa tushen "ka'idojin MDD", a sa'i daya kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su warware matsalolin da suke fuskanta ta hanyar yin shawarwarin siyasa, domin samun ci gaba tare.

A yayin da aka gudanar da babbar muhawara a gun babban taron MDD karo na 71, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, idan babu muhalli mai kyau na kwanciyar hankali, to akwai wuya matuka a cimma burin samun dauwamammen ci gaba, a saboda haka, kasar Sin tana son kiyaye ka'idojin MDD. Li Keqiang ya ce, "A cikin shekaru sama da 70 da suka gabata, al'ummun yawancin kasashen duniya suna jin dadin zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali, wannan ba abu mai sauki ba ne, shi ma ya nuna cewa, tsarin kasa da kasa na yanzu dake karkashin jagorancin MDD da ka'idar huldar kasa da kasa da aka tsara bisa tushen ka'idojin MDD sun dace da yanayin da kasashen duniya ke ciki, ya zama wajibi a kiyaye su yadda ya kamata. Dalilin da ya sa haka shi ne domin ba ma kawai hakan ya dace da moriyar al'ummun kasashen dunya ba, har ma zai samar da damammaki ga kasashen duniya da su cimma burin samun dauwamammen ci gaba. Ya kamata kasashen duniya su aiwatar da manufofin ka'idojin MDD, kuma su goyi bayan MDD da kwamitin sulhun MDD, ta yadda za su taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin kasa da kasa."

Shekarar bana ita ce ta cika shekaru 45 da aka maido da halaliyyar kujerar kasar Sin a MDD, ana ganin cewa, kasar Sin ta samu moriya daga wajen tsarin kasa da kasa da aka kafa bisa tushen ka'idojin MDD bayan yakin duniya na biyu, kana shekarar bana ita ce ta farko da aka fara aiwatar da jadawalin samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030.

Taken babban taron shi ne "Cimma burin samun dauwamammen ci gaba: sa kaimi kan ci gaban kasashen duniya." Li Keqiang ya sake bayyana manufar raya kasa ta gwamnatin kasar Sin wato samun dauwamammen ci gaba, ya ce, yayin da ake kokarin samun dauwamammen ci gaba, abu mafi muhimmanci shi ne samun bunkasuwa, a sa'i daya kuma wajibi ne a samu dauwamammen ci gaba, amma ba ci gaba kawai ba.

Yayin da yake halartar babban taron, Li Keqiang ya kira wani taron tattaunawa kan batun game da yadda za a tabbatar da jadawalin samun dauwammamen ci gaba nan da shekarar 2030 na MDD, inda ya yi bayani kan manufofin kasar Sin kan batun, da sakamakon da kasar Sin ta samu a wannan fannin, da sabbin matakan da kasar Sin ta dauka domin ingiza bunkasuwa a fadin duniya. Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta fara gudanar da ayyuka daga duk fannoni domin aiwatar da jadawalin ci gaba nan da shekarar 2030 na MDD, kuma ta fitar da shirin da ta tsara musamman ma domin cimma wannan burin.

Kan batun raya tattalin arzikin duniya bisa manyan tsare-tsare, Li Keqiang yana mai cewa, yanzu tattalin arzikin duniya yana fuskantar matsaloli da dama, shi ya sa ya yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya da su dauki matakai tare domin dakile su.

Game da habakar cudayar tattalin arzikin duniya, Li Keqiang ya yi kira ga kasashen duniya da su sanya kokari tare domin cimma burin yadda ya kamata. Ya ce, "A cikin shekaru sama da goma da suka gabata, kasashen duniya suna yin kokari tare domin kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, ko da yake wasu kasashe sun gamu da matsala, amma bai kamata ba a daina yin kokari, ya kamata a dauki matakai domin dakile matsalolin."

Kazalika, Li Keqiang ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen duniya su kara mai da hankali kan kasashen Afirka da sauran wasu kasashen dake fama da talauci mai tsanani, kuma su kara samar da taimako gare su, musamman ma a fannin raya masana'antu a kasashen.

Yayin da yake magana kan batutuwan da suka fi jawo hankulan al'ummun kasashen duniya, Li Keqiang ya bayyana cewa, ya fi kyau a warware sabane-sabane ta hanyar yin shawarwarin siyasa. Yana mai cewa, "Hakikanan abubuwa a tarihi sun shaida cewa, karfin tuwo zai kawo mana yake-yake kawai, ya kamata sassan dake gaba da juna su warware rikici ta hanyar yin shawarwarin siyasa."

A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya yaba da kokarin da babban sakataren MDD Ban Ki-moon yake yi da sakamakon da ya samu a cikin shekaru goma da suka gabata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China